Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Sojojin Najeriya Suka Yi Galaba Akan Mayakan Boko Haram A Neja


Sojojin Najeriya a Maiduguri a shekarar 2015.
Sojojin Najeriya a Maiduguri a shekarar 2015.

Bayanai dai na kara fitowa game da mummunar arangamar da jami’an tsaron sojin Najeriya suka yi da mayakan kungiyar Boko-Haram a yankin karamar hukumar Borgu ta Jihar Nejan Najeriya.

Rahotanni daga Najeriya na cewa, rundunar sojin kasar sun halaka akalla mayana Boko Haram takwas a jihar Neja da ke tsakiyar arewacin kasar.

Ko da yake, har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto babu wani karin haske daga jami'an tsaro na Najeriya akan wannan al’amari da ya faru a ranar Lahadin da ta gabata.

Amma rahotanni sun tabbatar da cewa, baya ga mayakan da aka kashe, sojojin Najeriyar sun yi nasarar cafke wasu manyan kwamandojin kungiyar biyu.

Kwamishin kula da harkokin tsaron cikin gida na Jihar Neja Mr. Emmanuel Umar ya tabbatar da aukuwar lamarin sannan ya bukaci jama’a su baiwa jami’an tsaro hadin kai.

Sojojin Najeriya a Maiduguri
Sojojin Najeriya a Maiduguri

Shugaban karamar hukumar ta Borgu Hon. Ahmed Baba Suleiman Yumu, ya ce mayakan na Bok Haram sun kai hari ne da nufin kubutar da ‘yan uwansu dake kulle a gidan yarin barikin sojin sama dake Wawa ta yankin Kainji, amma sai sojojin Najeriya suka samu nasarar kawar dasu.

Tuni dai gwamnatin Jihar Nejan ta yi kira ga jama’a da su kwantar da hankali domin ana daukar matakai akan lamarin kamar yadda sakataren gwamnatin Jihar Nejan Ahmed Ibrahim Matane ya bayyana mana.

Wannan al’amari dai yana zuwa ne kasa da mako daya da gargadin kasar Amurka ga Najeriya akan barazanar hare-haren ‘yan ta’adda a birnin Abuja fadar gwamnatin kasar dama wasu Jihohin da ke kusa da birnin na Abujan.

Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari

Yadda Sojojin Najeriya Suka Yi Galaba Akan Mayakan Boko Haram A Neja
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG