NIGER, NIGERIA - Bayanai dai sun nuna cewa rikicin ya barke ne a tsakanin wasu matasan kabilar Kambari da kuma wasu matasan kabilar Fulani, al’amarin da yayi sanadiyyar mutuwar akalla mutane biyu tare da kona ofishin ‘yan sanda da bankawa fadar sarkin garin wuta sannan kuma wasu gidajen Fulani da dama sunsha wuta.
Alhaji Abubakar Suleman Abara Dagacin garin na Salka da aka kona fadarsa ya ce har ya zuwa yammacin Talatan nan suna cikin wani yanayi na tashin hankali.
Bala Tajir Salka shi Dan Galadiman Salka ya ce rashin fahimtar junane aka samu a tsakanin matasan Fulanin da kuma na kabilar Kambari ya janyo lamarin. Gwamnatin Jihar Nejan dai ta tabbatar da aukuwar wannan al’amari.
Sakataren gwamnatin Jihar Alhaji Ahmed Ibrahim Matane ya ce duk da yake ya zuwa yanzu basu gama tantance yawan asarar da akayi ba a garin na Salka, amma sun kara tura karin jami’an tsaro a yankin domin tabbatar da dawo da zaman lafiya kamar.
A wani gefen kuma rundunar ‘yan sanda ta Jihar Nejan ta tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani asibitin gwamnati dake garin Gulu na yankin karamar hukumar Lapai.
A wata sanarwa da kakakin ‘yan sandan Jihar Nejan Wasiu Abiodun ya rabawa manema labarai, ya ce harin yayi sanadiyyar mutuwar mutun biyu tare da yin garkuwa da mutane takwas ciki harda wani jami’in kiwon lafiya.
Kwamishinan tsaron cikin gida na Jihar Neja Mr. Emmanuel Umar ya ce an kara tura karin jami’an tsaro a yankin na Gulu.
Saurari cikakken rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari: