Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TSARO: Gwamnatin Neja Ta Rufe Makarantun Firamare Da Sakandare


Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello (Hoto: Twitter, Gwamnatin jihar Neja)
Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello (Hoto: Twitter, Gwamnatin jihar Neja)

Rahotanni sun nuna cewa a yanzu haka akwai daruruwan makarantun firamare da sakandire da ke rufe a sakamakon matsalar ‘yan bindiga masu satar mutane domin neman kudin fansa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da masu fashin baki suke bayyana yankin arewacin Najeriya a matsayin wanda ya ke fuskantar koma baya a fannin ci gaban ilimi daga tushe, a daya gefen matsalar rashin tsaro da ya addabi wasu yankuna na yankin ya taikama wajan kara tabarbarewar Ilimin.

Jihar Neja da ke arewacin Najeriya na cikin jihohin da ke fama da wannan matsala ta 'yan bindiga da suka addabi wasu yankuna, inda bayanai suka nuna cewa akwai kimanin kananan hukumomi biyar da ala tilas hukumomin jihar suka rufe wasu makarantun firamare da sakandire saboda wannan matsala ta rashin tsaron.

Da yake jawabi ga manema labarai albarkacin ranar malamai ta duniya da aka gudanar a makon da ya gabata, Shugaban Hukumar dada Ilimai bai daya ta jihar Neja Alhaji Sa’idu Ibrahim, ya ce an rufe wadansu makarantu saboda halin tsaro.

“Ba za mu sake ba a zo a kwashe mana malamai a kwashe mana dalibai shi yasa aka rufe saboda wannan matsala ta tsaro,” in ji shi. “Kananan hukomomi biyar zuwa shida ne abun ya shafa da suka hada da Munya, Shiroro, Rafi, da wani gefe a Mariga, da Rijau da kuma wani dan bangare a Mashegun,”

Ko baya ga matsalar rashin tsaron akwai matsalar rashin kwararrun malamai da ke koyarwa a makarantun, al’amarin da ke kara maida hunnun agogo baya wajan ci gaban Ilimin.

A nashi bayanin, memba a Hukumar bada ilimin jihar Neja Alhaji Abdulkadi Shehu na Funtuwa ya ce gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti a karkashin kungiyar malamai ta kasar NUT da su fito su zakulo malamai wadanda suka cancanta da wadanda ba su cancanta ba a jihar Neja.

Ya kuma kara da cewa kuma wannan kwamiti ya zauna ya gama aikinsa har ya mika rahoto, an kuma zakulo wadanda ba su cancanci su zama suna aji ba.

A yanzu dai gwamnatin jihar Nejan ta ce tana daukar matakin kai daliban da aka rufe makarantunsu zuwa wuraren da babu matsalar rashin tsaron domin ci gaban karatunsu.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

XS
SM
MD
LG