Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

IBB, Abdulsalam Sun Bukaci ‘Yan Najeriya Su Hada Kai

Janar IBB Da Janar Abdulsalam Sun Bukaci ‘Yan Najeriya Da Su Hada Kai
Janar IBB Da Janar Abdulsalam Sun Bukaci ‘Yan Najeriya Da Su Hada Kai

A yayin da Najeriya ke cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai daga turawan kasar Birtaniya da suka yi wa kasar mulkin mallaka, tsofaffin shugabannin mulkin soja a kasar sun bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa a dunkule.

NIGER, NIGERIA - A ranar Asabar ne Najeriya ke cika shekaru 62 da zama kasa mai ‘yancin cin gashin kanta.

Tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce duk da yake an dan samu ci gaba amma da saura saboda haka ‘yan kasar su kara hakuri.

Janar IBB Da Janar Abdulsalam Sun Bukaci ‘Yan Najeriya Da Su Hada Kai
Janar IBB Da Janar Abdulsalam Sun Bukaci ‘Yan Najeriya Da Su Hada Kai

A wannan karon dai ranar zagayowar ‘yancin kan ya zo daidai da lokacin da Najeriya ke shirin tunkarar babban zabe, a saboda haka ne Janar Babangida ya ce yana fatan za a yi siyasa cikin nutsuwa babu tashin hankali.

Haka shi ma tsohon shugaban Najeriya, Janar Abdussalam Abubakar, ya yi tsokaci akan ranar samun ‘yancin na Najeriya.

Abdussalam wanda yake shugabantar cibiyar wanzar da lafiya a Najeriya, ya ce sun dauki matakin sanya hannu ne akan yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin ‘yan siyasa lokacin kamfe domin tabbatar da cewa an yi zaben lafiya.

Janar IBB Da Janar Abdulsalam Sun Bukaci ‘Yan Najeriya Da Su Hada Kai
Janar IBB Da Janar Abdulsalam Sun Bukaci ‘Yan Najeriya Da Su Hada Kai

Akan matsalar rashin tsaro da ya addabi sassan kasar kuwa, Janar Abdussalam ya ce duk ‘yan kasa suna da rawar takawa wajen shawo kan wannan matsala.

A yanzu dai ‘yan Najeriya na cike da fatar ganin an shawo kan matsalar rashin tsaron ta yadda ‘yan kasa za su samu sa’ida.

Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:

IBB, Abdulsalam Sun Bukaci ‘Yan Najeriya Da Su Hada Kai.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG