Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mutanen Wani Garin A Jihar Neja Bayan Halaka Wasu


Yan Bindiga
Yan Bindiga

Al’ummomin dake Garin Ibbi ta karamar hukumar Mashegu a jihar Nejan Najeriya da wasu kauyukan da ke kusa dasu na cikin wani yanayi na tashin hankali tare da zaman makoki bayan da wasu ‘yan bindiga suka halaka wasu mutanen yankin, suka kuma yi garkuwa da wasu.

NIGER, NIGERIA - Bayanai dai sun nuna cewa tun a farkon wannan wata na Ramadan ne wadan nan ‘yan bindiga suka tattara mutanen yankin da kawo yanzu ba a tantance yawansu ba, inda daga bisani suka halaka mutanen a safiyar jiya Alhamis bayan wani yunkuri na kubutar dasu da jami’an tsaro suka yi.

Sai dai gwamnatin jihar Nejan ta ce ‘yan bangan sun samu nasarar hallaka ‘yan fashin dajin da dama a wani karin bayani da Muhammad Bakar wani mazaunin garin na Ibbi ya yi.

Da yake tsokaci dangane da lamarin, Sakataren gwamnatin jihar Nejan Ahmed Ibrahim Matane ya ce duk da asarar rayukkan, an samu nasarar fatattakar ‘yan fashin dajin a wani karin bayani da ya yi mana.

Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:

‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mutanen Wani Garin A Jihar Nejan Najeriya Bayan Halaka Wasu.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

XS
SM
MD
LG