A baya-bayan nan ambaliyar ruwa ta yi barna sosai a jihohin Najeriya da dama, lamarin da ya shafi gonaki da gidaje ya kuma janyo hasarar rayuka a wasu wuraren. Jihohin da hukumar HYPPADEC ta fara bada tallafin sun hada da Kebbi, Neja, Kwara, Kogi, Binuwai, da kuma Filato.
Alhaji Abubakar Saddiq Yelwa Katukan Yauri, shi ne babban manajan hukumar HYPPADEC, ya ce ganin yadda al’ummar wadannan yankunan suka samu matsala sakamakon ruwan sama da aka yi ta shekawa, hukumar HYPPADEC ta tanadi shiri domin tallafa wa al’ummomin.
Ya ce hukumar zata tallafa da abinci, magunguna sabulai, kwanon gini, siminti, an kuma shirya likitoci domin su je wuraren da suka fuskanci bala'in ambaliyar domin kai taimakon gaggawa musamman ta fannin lafiya, daga baya kuma a duba taimakon da za a yi don kauda wadannan mutanen daga wuraren da ke tattare da hadarin ambaliyar" a cewar Saddiq.
Bayan haka hukumar HYPPADEC ta kuma sa masarautu, kananan hukumomi da kuma cibiyoyin tallafa wa jama’a na jihohi a cikin kwamitin da zai zauna domin tattauna tallafin da za a ba al’ummomin da abun ya shafa kuma a gaban jama’a za a yi komai. Kowacce al’umma zata zo da shugabanninta da matasanta a basu nasu kason domin tallafin ya kai ga al’ummar da abun ya shafa, a cewar Saddiq.
Daya ga cikin wadanda ambaliyar ruwan ta shafa a jihar Neja, Ibrahim Abubakar, ya ce al’amarin ya wuce duk tunanin mai tunani, sai dai su ce Allah ya mayar musu da Alheri.
A halin da ake ciki, akwai fargaba sosai na barkewar cututtuka a wuraren da ambaliyar tafi tsananta a sakamakon gurbacewar yanayi.
Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari: