Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zaben Jamhuriyar Nijar Na Yi Wa 'Yan Kasar Da Ke Zaune A Najeriya Rajista


Yan Jamhuriyar Nijar da ke zaune a jihar Neja, Najeriya
Yan Jamhuriyar Nijar da ke zaune a jihar Neja, Najeriya

Daruruwan 'yan kasar Janhuriyar Nijar dake zaune a Nigeria na ci gaba da yin tururuwa zuwa yin rujistar zabe da hukumar zaben kasar ta Nijar wato SENI ke gudanarwa.

Kimanin 'yan kasar Nijar 5000 ne ake sa ran za su yi rijistar zaben da zata basu damar kada kuri'a a Nigeria lokacin gudanar da zaben a can kasar ta Nijar.
Sai dai 'yan Nijar da Muryar Amurka ta tarar suna bin layin rijistar a birnin Minna sun ce lokacin da aka dibar masu ya yi kadan.
Yan Jamhuriyar Nijar da ke zaune a jihar Neja, Najeriya
Yan Jamhuriyar Nijar da ke zaune a jihar Neja, Najeriya
A hirar shida Muryar Amurka, babban jami'in hukumar zaben ta kasar Nijar dake aikin rijistar a jihar Neja , Abdu Amadu Ibrahim yace lokacin da aka dibar masu zai ishesu su kammala aikin rijistar.
Bayanai dai sun nuna cewa , idan ba a samu mutane 2000 ba a wannan rijista , 'yan Nijar dake jihar Neja zasu tafi Abuja ne domin kada kuri'a alokacin da za a gudanar da zaben.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00
XS
SM
MD
LG