Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dambarwa Tsakanin Sarkin Salka Da Al'ummarsa A Jihar Neja


Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello (Hoto: Twitter, Gwamnatin jihar Neja)
Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello (Hoto: Twitter, Gwamnatin jihar Neja)

Yayin da hukumomi a matakai daban-daban na Najeriya ke ci gaba da janyo hankalin ‘yan kasar akan muhimmancin ‘yin babban zaben kasar cikin kwanciyar hankali da zaman Lafiya, ba haka take ba a garin Salka dake Jihar Neja.

NIGER, NIGERIA - Al’ummar garin na Salka dake yankin karamar hukumar Magama a Jihar Nejan Najeriya, sun nuna damuwa ne akan yadda suka ce sarkin garin baya daukar matakin zaman Lafiya a tsakanin al’ummar da ya ke shugabanta.

Tun a kwanakin baya anyi wani tashin hankalin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutun biyar tare da kona kimanin gidaje 50, wanda a ciki har da ofishin ‘yan sanda da kuma gidan basaraken garin, al’amarin da ya sa sarkin garin ya yi gudun hijira.

A wani taron manema labarai da al’ummar garin Salkan suka gudanar a Minna, sun yi kira ga sarkin Sudan na Kontagora da ya hanzarta daukar mataki na dakatar da wannan Dagaci dake karkashin Masarautarshi.

Shugaban wata kungiyar matasa a garin na Salka, Malam Shu’aibu Alkali ya ce tun da Sarkin na Salka ya na zaman gudun hijira, to suna bukatar ya ci gaba da zama a can.

Alhaji Abubakar Abara shine Sarkin na Salka wanda ake korafi akan shi ya baiwa al’ummar da yake shugabanta hakuri.

To ita ma dai masarautar Kontagora ta ce tana sane da wannan dambarwa dake tsakanin mutanen wannan gari da sarkin na su, kuma suna daukar matakin shawo kan lamarin.

A halin yanzu dai Jama’a na cike da fatan ganin an shawo kan wannan zaman tankiya a tsakinin wannam Sarki da jama’arsa a wannan yanki da ke fama da matsalar ‘yan bindiga.

Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:

 Al’ummar Salka A Jihar Nejan Najeriya Na Neman A Shiga Tsakaninsu Da Sarkinsu.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG