Biyo bayan zarge zargen da ake yiwa kasar China cewa ta bude ofishin ‘yan sanda a Najeriya, zargin da ofishin jakadancin China a Abuja ya karyata, duk da haka masana da kwararru a Najeriyar na cewa lalle a gudanar da bincike.
Babban hafsan hafsoshin rundunar tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor ya ce rikicin mayakan Boko Haram yayi sanadiyyar mutuwar mutane dubu dari wasu miliyan biyu kuma sun kauracewa matsugunnansu, bayan asarar dukiya da aka yi.
Dakarun runduna ta dari da hamsin da biyar dake cikin dakarun OPERATION HADIN KAI da ke yaki da Boko Haram a shiyyar arewa maso gabas na gumurzu da 'yan ta'addan ISWAP a yankin Baman jihar Borno.
Yayin da ake ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro a Najeriya gwamnatin kasar ta tsara kashe naira tiriliyan daya da biliyan talatin da biyar don fuskantar matsalar tsaro a shekarar 2023.
A wani taron manema labarai da aka yi ranar Alhamis, shelkwatar tsaron Najeriya ta yi karin haske kan hanyar da aka bi wajen kubutar da sauran fasinjojin jirgin kasan nan da suka rage a hannun ‘yan ta’addan Boko Haram.
A wani matakin tunkarar kalubalen tsaro da ya ke naso a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya da ma wasu jihohi bakwai da ke makwabtaka da ita, mahukunta sun kaddamar da wani shirin kawo karshen matsalar.
Hukumar dake kula da ayyukan yansandan Najeriya ta kori wasu manyan ‘yan sanda bakwai daga bakin aiki tare da rage mukaman wasu ‘yan sandan.
Rundunar sojojin Najeriya ta ja kunnen masu rura wutar rikici a sassa daban daban na kasar da su yiwa kansu kiyamullayli, domin kuwa rundunar zata dau duk wani matakin da ya dace kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya bata wajen ganin ta kare yan kasa na gari.
Ana zargin farfesa Zainab Dinne da wata mai mata aikin gida Rebecca Enechido da kuma wani mutum da laifin cin mutuncin 'yar sandar da raunata ‘yar sanda mai tsaron lafiyarta.
Jiragen yakin sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta a sansanonin hatsabinin dan bindigar nan Bello Turji su ka kashe mutanensa da dama.
Yayin da hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya ta DSS ta nemi wata babbar kotun tarayya ta ba ta damar ci gaba da tsare mawallafin jaridar Desert Herald Mallam Tukur Mamu har tsawon kwanaki 60, lauyoyin Mamu sun ce babu abun fargaba gaskiya z ata yi halinta.
Jami'an hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya ta DSS sun kai wani samame a gidan surikin mawallafin jaridar Desert Herald Mallam Tukur Mamu da tsakar daren ranar Alhamis inda suka yi awon gaba da shi zuwa ofishinsu.
Malam Mamu ne ya shiga tsakani wajen karbo kusan mutum 20 daga cikin fasinjojin jirgin kasa da ‘yan bindiga suka sace a watan Maris din wannan shekara.
A baya, ya taba shaidawa Muryar Amurka cewa ya janye daga shiga tsakani a kokarin kubutar da sauran fasinjojin jirgin kasa da aka sace, saboda abin da ya kira barazana da rayuwarsa take fuskanta.
Hafsan hafsoshin sojin Najeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya ya bayyana cewa, za a yi amfani da dokar kasa wajen hukumta sojan da ya kashe limamin addinin Islama a jihar Yobe
Yayin da lamarin tsaro ke ci gaba da ta’azzara a wasu sassan Najeriya, rundunar mayakan ruwa na taka muhimmiyar rawa wajen ganin an samar da zaman lafiya a ciki da wajen kasa.
A ci gaba da samun nasara da sojojin Najeriya ke yi a baya bayan nan, dakarun Operation Hadarin Daji da ke aiki a arewa maso yammacin Najeriya, sun damke wasu miyagu da su ka shigo daga kasashen ketare.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce an sake damko karin wasu yan ta'adda guda biyu dake cikin maharan da suka kai harin cocin Owo
Shi dai wannan kwamanda na Boko Haram shi ne wanda a shekarar 2014 ya jagoranci kai farmakin da ya yi sanadin kashe daruruwan mutane a garin Bama tare da maida garin karkashin ikon abin da suka kira Daularsu
Domin Kari