ABUJA, NIGERIA - Wata sanarwa da Ma'akatar Harkokin Wajen Amurkan ta fitar na cewa zata rage jami'anta da aikinsu ba na gaggawa ba ne tare da iyalansu don maida su gida bisa abin da ta kira yiwuwar kai wani gagarumin harin ta'addanci a babban birnin tarayyar Najeriya.
Tuni kuma gwamnatin Najeriyar ta bakin Ministan watsa labarai Alhaji Lai mohammed ta maida martani cewa “Amurka na da ‘yancin ta ce su koma gida in suna so, amma mu a matsayinmu na kasa alhakinmu ne mu tsare kasar, kuma wannan mataki na Amurka ko kadan ba zai tayar mana da hankali ba. “
“Koma mene ne wata gwamnati za ta gaya wa mutanenta, sau nawa ake samun harbe-harbe a makarantun Amurka? Sau nawa ake samun kashe kashe a Amurka? Sun iya hasashen wace makaranta ce ta gaba da ‘dan bindiga zai bude wuta akan kananan yara? Yanzu ‘yan Najeriya dake Amurka suma basa fuskantar matsalar tsaro ne? Haba!'
Shi ma kwamishinan ‘yan sanda na birnin Abuja, Sunday Babaji, ya ce tun ma kafin yanzu suna nan cikin shirin ko ta kwana inda jami'ansu na fili da na boye ke aiki ba dare ba rana don tabbatar da tsaro a baki dayan yankin babban birnin tarayya.
Saurari cikakken rahoton daga Hassan Maina Kaina: