ABUJA, NIGERIA - Hukumar Kula da ayyukan ‘yan sandan Najeriyar, wacce ta shafe kwanaki tana gudanar da taronta karo na goma sha biyar a birnin Abuja, ta amince da korar wasu manyan Jami'an ‘yan sanda bakwai da kuma rage mukaman wasu manyan jami'ai goma.
Mai magana da yawun hukumar Ikechukwu Ani ya fada a wata sanarwar da ya sanya wa hanu cewa hukumar ta ja kunnen wasu ‘yan sanda goma sha uku kana za a bai wa wasu biyu kuma takardun gargadi yayin da ta wanke wasu guda hudu.
Hukumar dai ta dau wannan mataki ne a matsayin wani bangare na ladabtarwa akan jami'an da aka samu da wuce gona da iri wajen tafka laifi yayin gudanar da ayyukansu.
Wannan mataki dai tuni ya ja hankalin kwararru da masana tsaro irinsu Dr. Kabiru Adamu da ke ganin dacewar abin, inda ya ce akwai gibi sosai na rashin aminci tsakanin ‘yan sanda da jama'a fararen hula.
Shi ma mai sharhi akan al'amuran yau da kullum Dr. Farouk BB Farouk wanda ya yaba wa hukumar amma ya ce akwai bukatar nan gaba a bayyana sunayen jami'an da kuma irin laifin da suka yi.
Saurari cikakken rahoton daga Hassan Maina Kaina: