Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abinda Hafsan Hafsohin Sojin Najeriya Ya Ce Game Da Kashe Sheikh Aisami


Hira da Babban Hafsan sojojin Najeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya
Hira da Babban Hafsan sojojin Najeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya

Hafsan hafsoshin sojin Najeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya ya bayyana cewa, za a yi amfani da dokar kasa wajen hukumta sojan da ya kashe limamin addinin Islama a jihar Yobe

A hirar shi da shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka, Aliyu Mustapha Sokoto, Hafsan Hafsohin ya ce, bisa ga tsarin dokar aikin soja, idan wani jami’I ya aikata babban laifi da aka tabatar da haka, kafin a hukumta shi a kotu, mataki na farko da ake dauka na kare kimar aikin shi ne sallamar shi daga aiki sabili da gudun kada ya bata wa rundunar suna.

Ya bayyana cewa, abinda sojan ya aika ba tarbiyar sojoji ba ne. Bisa ga cewarshi, akwai akidoji biyar da ake koyawa duk wanda ya shiga soja kafin ya fara yin komi, da suka hada a karfin zuciya, da biyayya, da mutunta kowa. Saboda haka dukan jami’an soja sun san yadda ya kamata su kula da kowa su kuma mutunta kowa.

Bisa ga cewarshi, akan samu baragurbi a ko’ina, sannan idan an same su, ba shiru za a yi ba. Ana bin ka’idoji da kuma dokokin da suka dace wadanda doka ta shinfida amma ba a jan kafa a kan wannan.

Laftanar Janar Yahaya ya bayyana cewa, kafin wannan, an taba samun wadansu sojoji da su ka aikata irin haka a Maiduguri aka kafa kutun soja ta musamman ta hukumta su.

Hira da Babban Hafsan sojojin Najeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya
Hira da Babban Hafsan sojojin Najeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya

Matsalar tsaro

Dangane da matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya, hafsan hafsohin ya bayyana cewa, “ba a Najeriya kadai ake fama da matslar tsaro ba, matsala ce da ta shafi kasashe da ke makwabta da Najeriya da kuma sauran kasashen duniya sabili da yadda duniya ta zamo tamkar gari guda. Bisa ga cewarshi, ana samun nasara kwarai a fannin yaki da kungiyar Boko Haram da aka yi fama da ita a Najeriya. Yace akasin yanayin a lokutan baya, yanzu ana iya walwala a kusan dukan sassan arewa maso gabashin Najeriya inda kungiyar tafi tada kayar baya.” Yace an bubbude makarantu, kasuwanni suna ci ko’ina, kuma wadanda su ke ajiye makamai suna fitowa.

Yace yanzu an samu a kalla wadanda sun kai dubu 70, cikinsu, kusan dubu ishirin duka mayaka ne na Boko Haram da su ka ajiya makamai wadanda su ka fahimci cewa, abinda su ke so, babu nasara a ciki. Da aka tambaye shi ko kashi nawa ne zai iya cewa na ‘yan Boko Haram su ka rage, sai ya bayyana cewa, ba za a iya cewa ga ainihin adadin wadanda su ka rage ba sabili da yanayin tsaro yana da wuya a iya tantance wannan.

Babban hafsan sojin ya ce yanzu, za a yi kwanaki ba tare da jin wani abu ya faru ba. Sai dai inda jefi -jefi akan samu wadansu tsirarru da su ke neman abinci su kaiwa mutane hari da suka san basu da makamai. Bisa ga cewarshi, ko da ana zaman lafiya, ana iya samun irin wannan yanayin nan da can.

Wata maboyar mayakan Boko Haram/ISWAP da dakarun Najeriya suka tarwtasa Facebook/Nigerian Army (Mun yi amfani da wannan hoto don misali ne)
Wata maboyar mayakan Boko Haram/ISWAP da dakarun Najeriya suka tarwtasa Facebook/Nigerian Army (Mun yi amfani da wannan hoto don misali ne)

Yaki da ISWAP

Da aka tambaye shi abinda ya banbanta yaki da Boko Haram da kuma ISWAP sai babban hafsan sojin ya bayyana cewa, a umarnin su, duk wanda ya ke dauke da bindiga, ba a tsayawa ana bayani da shi, “domin duk wani da ya dauki makamai ya fuskanci Najeriya to makiyin Najeriya ne.” Ya ce, a can Arewa Maso Gabashin Najeriya, ana samun ‘yan Boko Haram da ISWAP, da ma ‘yan baranda. Duk wani da ya dauki makami, ya fuskanci kasar sa, ko da ba can ba, ko nan ne, ko yace shi mai garkuwa da mutane ne ko dan bindiga ne, ba ruwanmu ba mu tsayawa muna tambaya.”

Masu Garkuwa Da Mutane

Dangane kuma da masu garkuwa da mutane da neman kudin fansa, da aka tambaye shi ko yana gani ‘yan Boko Haram ne suka rikide suka sake salon kaiwa al’umma hari sai yace, “tun dama akwai mutane masu tada hankalin al’umma da aikata irin wadannan miyagun ayyuka, sai dai daga baya abin ya kara zafafa, amma dama ana samun irinsu.”

Ya bayyana cewa, yadda duniya ta zama karamin gari, haka su ma ‘yan ta’adda suna da nasu alaka, wadanda suna haduwa har su koyi wadansu abubuwa da ke faruwa a wadansu wurare.

Yace akwai yiwuwar irin yakin da suka yi da ‘yan kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, ya sa wadansu tsiraru suka gudu zuwa wadansu sassan kasar su ka je suka hada kai da wadansu har su koyi abubuwan da ke faruwa a wadansu wurare.

Fulani masu garkuwa da mutane
Fulani masu garkuwa da mutane

Hafsan hafsoshin yace, yana yiwuwa tsananin yakin da su ka yi a Arewa maso gabashin kasar yasa wadansu suka gudu suka je suka hada kai da wadansu su cakude. Ya bayyana cewa, rashin zaman lafiya da rashin tsaro da wadansu dalilai ya sa wadansu ‘yan baranda suka shiga ayyukan ta’addanci.

Matsalar tsaro a jihohin Arewa maso yamma

A bayaninsa dangane da abinda rundunar sojin Najeriya ke yi dangane da matsalar tsaro da ake fama da ita a jihohin arewa maso gabashin Najeriya da suka hada da Sokoto, Zamfara, Kaduna, Katsina, Naija da sauransu, sai laftanar janar Faruk Yahaya ya bayyana cewa, tilas ne jami’an tsaro su kakkabe ‘yan ta’addan daga ko’ina a fadin kasar saboda haka ba za su yi kasa a guiwa ba wajen dakile ayyukan maharan.

Yace yanzu haka lamura sun fara daidaita sabili da dukan bangarorin aikin soja da suka hada da mayakan ruwa da na sama da sauransu sun hada karfi da karfi kuma suna samun nasara. Ya bayyana cewa, suna iya sauya tsarin aiki da kuma yanayin aikinsu ya yi daidai da lamarin da ake fuskanta domin kwalliya ta biya kudin sabulu.

Saurari abinda Hafsan Hafsoshin ya ce dangane da kashe Sheikh Aisami:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG