Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ayyukan Boko Haram Sun Yi Sanadin Mutuwar Sama Da Mutum Dubu Dari A Najeriya-Janar Irabor


Janar Lucky Irabor (Facebook/Nigeria Defense)
Janar Lucky Irabor (Facebook/Nigeria Defense)

Babban hafsan hafsoshin rundunar tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor ya ce rikicin mayakan Boko Haram yayi sanadiyyar mutuwar mutane dubu dari wasu miliyan biyu kuma sun kauracewa matsugunnansu, bayan asarar dukiya da aka yi.

Janar Irabor wanda ke magana a yayin wani taron bita da fadar shugaban Najeriya ta shirya a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, ya ce rikicin ya kuma janyo asarar kimanin dala miliyan dubu tara.

Babban hafsan ya ce dakarun kasar sun iya takaita ayyukan ‘yan ta’addan Boko Haram a sassan yankin Arewa maso gabashin Najeriya, ko da yake yanzu wasunsu na sulalewa zuwa yankin Arewa maso yammacin kasar.

Ya ce cikin shekaru bakwai da suka gabata, gwamnati ta kashewa dakarun kasar makudan kudade, shi ya sa dakarun ke kara taka rawa wajen aikin samar da tsaro na cikin gida.

Da yake tsokaci a game da matsalar satar mai a yankin Niger-Delta, Irabor ya ce wasu tsageran da ke tada kayar baya a yankin ne suka rikide zuwa barayin mai, al’amarin da ke nuna akwai gibi a tsarin tsaron kasar.

Domin cike wannan gibi, ya zama dole a samar da kyakkyawan shugabanci, da inganta karfin soji, da kuma sauya halayya daga ‘yan kasa a cewar babban hafsan.

Masana harkar tattalin arziki daga Arewa maso gabas irinsu Abubakar Ali, na ganin adadin asarar da aka tafka ya wuce yadda babban hafsan ya bayyana duba da irin barnar da ‘yan ta’addan suka dauki shekaru suna yi a yankin musamman ta fannin kasuwanci.

Daya daga cikin shugabannin ‘yan kasuwar Arewacin Najeriya Alhaji Isa Sakatare da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya, ya ce tun da yanzu gwamnati ta lura da irin asarar da aka tafka a yankin to akwai bukatar hukumomi su tsara yadda za a taimaka wa ‘yan kasuwar yankin.

Ga sautin rahoton Hassan Maina Kaina Daga Abuja:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG