BORNO, NIGERIA - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fara binciken harin da ake zargin cewa wasu ‘yan bangar siyasa sun kai kan tawagar tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya kuma ‘dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar, a birnin maiduguri na Jihar Borno.
Amma rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta karyata maganar inda mai magana da yawun rundunar ya ce zargin bai da tushe balle makama, kuma kakakin ‘yan sandan na Jihar Borno Kamilu Sharubutu ya ce zargin wani yunkurin haddasa rudani ne a Jihar.
To amma cikin wani abu mai kama da martani mai marwara, Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya amince cewa lalle an kai wannan farmaki inda ya ci gaba da cewa ''Lallai abin da ya faru a Borno ya faru, kakakin ‘yan sandan na Borno ya yi gaggawar yin martani akan batun, don haka za a yi bincike na kwakwaf don gano abin da ya faru da zummar hana aukuwar haka nan gaba''
Tuni kuma jam'iyyar PDP ta yi na'am da wannan mataki, inda mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, Ambasada Umar Iliya Damagum ya nemi lallai a yi bincike na hakika kuma a ladabtar da duk masu hannu cikin wannan lamari.
Saurari cikakken rahoton daga Hassan Maina Kaina: