Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Saman Najeriya Na Cigaba Da Kai Farmaki Kan Mayakan ISWAP


Janar Farouq Yahaya
Janar Farouq Yahaya

Dakarun runduna ta dari da hamsin da biyar dake cikin dakarun OPERATION HADIN KAI da ke yaki da Boko Haram a shiyyar arewa maso gabas na gumurzu da 'yan ta'addan ISWAP a yankin Baman jihar Borno.

Bayanan da wakilin Muryar Amurka ya tattaro daga filin daga na nuna cewa, an soma gumurzun tun jiya da yamma akan hanyar Kumshe zuwa Banki.

Sojojin dai sun sami rahoton sirri ne daga wasu kauyawa na inda aka ga 'yan ta'addan na tattaruwa a wani wuri kusa da bakin hanya suna shirye shiryen kai harin ta'addanci.

Dakarun dai bayan samun bayanan sun nausa wurin cikin kuzari inda suka fara bata kashi tsakanin bangarorin biyu.

Sojojin daga bisani sun yi nasara akan 'yan ta'addan su ka kashe mayakan ISWAP din guda shidda yayin da sauran suka tsere cikin daji wajajen Gauri da Gargash inda suka kuma tsara kai wani farmakin a Mayinti da Darajamal

Daga bisani dai sojojin saman Najeriya sun yi amfani da jiragen yakin nan samfurin A29 SUPER TUCANO, inda suka auna dandazon mayakan na ISWAP kuma ba a kuskure ba.

Hedkwatar rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da wannan farmaki inda tace nan gaba ne zatayi cikakken karin bayani akai

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG