Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da Lauyoyin Tukur Mamu Suka Ce Kan Umarnin Ci Gaba Da Tsare Shi


Jami'an DSS a Najeriya (AP)
Jami'an DSS a Najeriya (AP)

Yayin da hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya ta DSS ta nemi wata babbar kotun tarayya ta ba ta damar ci gaba da tsare mawallafin jaridar Desert Herald Mallam Tukur Mamu har tsawon kwanaki 60, lauyoyin Mamu sun ce babu abun fargaba gaskiya z ata yi halinta.

ABUJA, NIGERIA - Biyo bayan bukatar da hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya ta gabatar ta neman kotu ta sahale mata damar ci gaba da tsare mawallafin jaridar Desert Herald Mallam Tukur Mamu, lauyiyonsa sun magantu.

Hukumar DSS ta shaida wa kotun cewa duba da bukatar zurfafa binciken da ake yi wa Mamu, ya dace a ba ta karin lokaci akalla zuwa kwana sittin don aiwatar da binciken.

Lauyan hukumar DSS Hamza Pandogari, a cikin takardar da ya mika wa kotun, ya ce 'yan sandan kasa da kasa ne suka kama Mamu a filin jirgin saman Birnin Alkahira akan hanyarsa ta zuwa Saudiyya.

Ya ci gaba da cewa, bayan da aka dawo da shi Najeriya hukumar ta nemi izinin kotu da ta gudanar da bincike a gida da ofishinsa, kuma bayan kaddamar da binciken ta ce ta gano kudaden kasashen waje da sauran ababen da ka iya zama shaida.

A saboda haka ta nemi kotun ta ba ta zarafin ci gaba da tsare Malam Mamu har tsawon wata biyu don karin bincike.

Tuni kuma kotun a karkashin Mai shari’a Evelyn Maha, ta amince da wannan bukata.

Sai dai kuma lauyoyin Tukur Mamun sun shaida wa Muryar Amurka cewa duk da iyalan wanda suke karewa ba su cika so ana magana akan batun ba da a halin yanzu ke gaban kotu, amma sun ce babu wani abin fargaba, don suna da yakini a karshe gaskiya za ta yi halinta.

Lauyoyin na Mallam Mamu sun bayyana cewa bisa kundin tsarin mulkin Najeriya, duk wanda ake zargi ba mai laifi bane har sai kotu ta tabbatar da laifi akansa, don haka sun nemi hukumar DSS ta dakatar da yadda take nuna wanda suke karewa tamkar mai laifi. Suna masu jan hankalin hukumar DSS da ta bi doka da oda.

Lauyoyin Mamu sun kuma nemi Jama'a musamman masu azarbabin yin sharhi da su daina sakin baki kan batun ganin har yanzu maganar na a matakin bincike.

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG