Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ofishin Jakadancin China A Najeriya Ya Karyata Labarin Bude Tashar 'Yan Sanda Na China A Najeriya


Jami'in China Da 'Yan Jarida
Jami'in China Da 'Yan Jarida

Biyo bayan zarge zargen da ake yiwa kasar China cewa ta bude ofishin ‘yan sanda a Najeriya, zargin da ofishin jakadancin China a Abuja ya karyata, duk da haka masana da kwararru a Najeriyar na cewa lalle a gudanar da bincike.

Wata kungiyar dake rajin kare hakkin bil'adama mai siuna HURIWA ta nemi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya yiwa ‘yan kasar bayani dangane da labaran dake yawo a kasar cewa kasar China ta kafa ofishin ‘yan sanda a Najeriyar.

Huriwa ta ce wannan batu in har ya tabbata gaskiya to zai bata mamaki inda take aza alamar tambaya shin ko Najeriya ma nada ofishin ‘yan sanda a can kasar ta china? ta kara da cewa hakan bai gaza cin amanar kasa da yiwa ‘yanci da diyaucin Najeriya karan tsaye.

Wannan zargi dai da a halin yanzu ke ci gaba da jan hankalin ‘yan Najeriya, tuni masana da kwararru ke ganin biri ya yi kama da mutum don haka suka nemi jami'an tsaro su gaggauta gudanar da bincike don gano gaskiyar abin dake faruwa.

A bangarenta, kasar China ta yi watsi da wannan zargi inda cikin sanarwar da ta fitar, take cewa ba gaskiya bane batun wai ta kafa caji ofis a Najeriya, ta ce bata da kuma niyar hakan, amma abin da kawai ke faruwa shine ta kafa ofishin tuntuba ne don amfanin sinawan dake
Najeriya.

To sai dai kuma a cewar wani tsohon jami'in diflomasiyya Nassir Zaharadden, yadda ‘yan China ke tafiyar da harkoki a Najeriya musamman in aka yi la'akari da yadda ‘yan kasar basa bin dokar kasar to komai ka iya faruwa, ya ce nan baya kadan wani dan Sin ya kashe wata ‘yar Najeriya a Kano, da kuma yadda suke aikin hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba.

Ya ce tun da aka kafa huldar jakadanci tsakanin Nigeriya da China shekaru hamsin da daya da suka gabata dangantakar kasashen biyu bata inganta sosai ba sai bayan dawowa mulkin dimokaradiyya a 1999, yanzu dai akwai kimanin ‘yan kasar China dubu goma a Najeriya dake gudanar da harkokinsu.

Shima kwararren lauyan tsarin mulki Barrister Yakubu Saleh Bawa, ya ce in har wannan magana ta tabbata, to kuwa abin akwai mamaki matuka. Yana cewa kada a dauiki wannan magana da wasa duk da ofishin jakadancin China a Najeriya yayi watsi da batun.

Barrister Yakubu Sale Bawa ya ce ya kyautu zaratan jami'an ‘yan sandan Najeriya da na DSS su kaddamar da binciken hadin gwiwa don bankado gaskiyar magana, kuma duk wanda aka samu da aikata ba daidai ba a hukuntashi

Ga sautin rahoton Hassan Maina Kaina daga birnin Abuja:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

XS
SM
MD
LG