Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsaro: Sufeta Janar Na ‘Yan Sandan Najeriyar Ya Bada Umurnin Gudanar Da Atisaye Na Kwana Biyu A Abuja


IGP Alkali Baba Usman
IGP Alkali Baba Usman

Biyo bayan gargadin da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya yi cewa ta yiwu a sami harin ta'addanci a Abuja babban birnin tarayyar kasar, sufeta janar na ‘yan sandan Najeriyar, Usman Alkali Baba, ya bada umarnin gudanar da wani atisayen zaratan ‘yan sandan Abuja na kwana biyu.

ABUJA, NIGERIA - Atisayen wanda yansandan sashin yaki da ta'addanci da kuma na bangaren kwantar da tarzoma zasuyi a ranekun talata ashirin da biyar da laraba ashirin da shida ga watannan na oktoba zai kunshi harbe harben bindiga da nuna karfin tsaro irin na tauna tsakuwa don a baiwa aya tsoro.

CSP Almustapha Sani na sashin hulda da jama'a a hedkwatar yansandan Najeriyar ya shaidawa muryar Amurka cewa sufeta janar ya kuma baiwa kwamishinan yansandan birnin Abuja da na sauran jihohi shida dake makwabtaka da Abujan dasu kara tashi tsaye don sake salon tsaron tunkarar matsalar tsaron.

Yayin da ya ke tabbatar da cewa a bangarensu, hedkwatar 'yan sandan kasar, zai ba su duk wani goyon baya don tabbatar da tsaron dukiyar jama'a da rayukansu ba tare da wani mishkila ba.

Shi ma ministan Abuja, Mallam Muhammad Musa Bello ya kira taron gaggawa irin na tsaro da kusoshin tsaron birnin inda ya jadda kudirin gwamnati na tsare babban birnin tarayyar kasar.

Mallam Muhammad Musa Bello ya ce hukumar raya birnin Abuja ba za ta rufe makarantu a birnin ba saboda fargabar tsaro, ya kuma bada umarnin bude wadanda ma aka rufe din nan take.

To saidai kuma, yayin da mahukunta ke kai komo akan wannan gargadi na Amurka, su kuwa talakawa a birnin Abujan ba abin da ya dame su, domin kusan duk wadanda Muryar Amurka ta tuntunbuba sun ce su ba su ma da labarin wannan gargadi na Amurka.

Al'amarin da ke nuna wannan gargadi yafi tasiri akan 'yan boko da ‘yan siyasa da kusoshin gwamnati, kasancewar talakawan na ci gaba da gudanar da hada hadarsu ta yau da kullum a duk bangarorin rayuwa

Saurari cikakken rahoton daga Hassan Maina Kaina:

Sufeta Janar Na ‘Yan Sandan Najeriyar Yabada Umarnin Gudanar Da Atisaye Na Kwana Biyu A Abuja.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

XS
SM
MD
LG