Da yake amsa tambaya akan yadda aka kubutar da sauran fasinjojin jirgin kasan da suka rage a hannun 'yan ta'adda, daraktan cibiyar samar da bayanai kan arangamar da dakarun Najeriya ke yi Manjo Janar Musa Danmadami, ya ce babban abu mai muhimmanci shi ne an kubutar da fasinjojin.
"A irin wannan aiki ana amfani da karfin soji ko hanyar da ba ta karfin soji ba, a wannan yanayin ba a yi amfani da karfin soji ba shi ya sa aka samu nasarar kubutar da fasinjojin salin alin," a cewar Janar Danmadami.
Janar din ya kuma bayyana cewa rundunar tsaron Najeriya tare da hadin gwiwar wasu hukumomin gwamnati, da kwamitin aiki da cikawa sun yi kokari wajen kubutar da fasinjojin jirgin kasan da suka share wata shida a hannun ‘yan ta'adda.
Shi ma daraktan yada labarai na shelkwatar tsaron Najeriyar Manjo Janar Jimmy Akpor, ya ce a irin wannan yanayin ana amfani da wasu matakai biyu ne don cimma muradin karfin kasa, kuma ana amfani da matakan ne a lokaci guda ko lokuta dabamdaban.
Janar Akpor ya ce wasu matakai na sirri aka bi wajen samun nasarar kubutar da ‘yan ta’addan, ya kuma tabbatar da cewa duk wanda ya yi wa kasa laifi to lallai za a kamo shi komai daren dadewa don ya fuskanci hukunci.
Saurari rahoton Hassan Maina Kaina daga Abuja: