Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahukunta Sun Kaddamar Da Wani Shirin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya

Mahukunta Sun Kaddamar Da Wani Shirin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya
Mahukunta Sun Kaddamar Da Wani Shirin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya

A wani matakin tunkarar kalubalen tsaro da ya ke naso a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya da ma wasu jihohi bakwai da ke makwabtaka da ita, mahukunta sun kaddamar da wani shirin kawo karshen matsalar.

ABUJA, NIGERIA - Da yake magana da Muryar Amurka dangane da wannan mataki, kwamishinan ‘yan sandan Abuja, CP Babaji Sunday, ya ce gamayyar jihohin sun hada da Kaduna, Neja, Nasarawa, Filato, Benue, Kogi da Abuja.

Mahukunta Sun Kaddamar Da Wani Shirin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya
Mahukunta Sun Kaddamar Da Wani Shirin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya

Kwamishinan ‘yan sandan na Abuja ya ce matsalar satar mutane da aika- aika irin na ‘yan bindiga ne ya zaburar da mahukunta na farfado da wannan mataki don hada karfi da karfe a ga cewa an yi wa tufkar hanci.

An dai kaddamar da wannan hadaka ce a sansanin bataliya ta 176 da ke Kwali yankin kan iyakar Abuja da Jihar Kogi, kuma baya ga ‘yan sanda, akwai kuma sojojin kasa, sojin ruwa, sojin sama, jami'an hukumar DSS da na Civil Defense da dai sauran hukumomin tsaro.

Mahukunta Sun Kaddamar Da Wani Shirin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya
Mahukunta Sun Kaddamar Da Wani Shirin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya

CP Babaji Sunday ya kara da cewa, yanzu da wannan hadaka jami'an tsaron za su yi aiki kafada da kafada a dukkannin jihohi bakwai da Abujan wajen ganin an fatattaki miyagun da ke hana jama'a zaman lafiya a wadannan yankuna

Saurari cikakken rahoto daga Hassan Maina Kaina:

Mahukunta Sun Kaddamar Da Wani Shirin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG