Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan sandan Kasa Da Kasa Sun Kama Tukur Mamu A Masar


Tukur Mamu
Tukur Mamu

A baya, ya taba shaidawa Muryar Amurka cewa ya janye daga shiga tsakani a kokarin kubutar da sauran fasinjojin jirgin kasa da aka sace, saboda abin da ya kira barazana da rayuwarsa take fuskanta.

Rundunar ‘yan sandan kasa da kasa wato Interpol ta cafke Alhaji Tukur Mamu, tsohon mai shiga tsakani a kokarin kubutar da fasinjojin jirgin kasan nan da aka sace a watan Maris, wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna.

An kama Mamu ne a birnin Alkahira na kasar Masar a ranar Talata kamar yadda kaninsa Alkali Mamu ya tabbatarwa Muryar Amurka.

A cewar Alkali, jami'an tsaron sun kama yayan nasa ne a filin jirgin saman birnin Alkahira a yayin da yake jiran jirgi domin tafiya kasar Saudiyya inda zai gabatar da aikin Umrah.

Alkali ya ce, Tukur Mamun na tafiyar ne da matansa, yaransa da wani dan'uwansa a lokacin da ‘yan sandan suka tsare shi, sun kuma maido da shi Najeriya bayan sun mai tambayoyi ba tare da samunsa da wani laifi
ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Mamu yana cewa an saka shi a wani jirgi don ya maido da shi Najeriya.

"Ba na fargabar komai." Mamu ya fadawa Daily Trust a hira ta musamman da ta yi da shi.

Malam Tukur Mamu shi ke rike da mukamin sarautar gargajiya ta Dan
Iyan Fika.

Har ila yau shi ne shugaba kuma mawallafin jaridar Desert Herald da ake bugawa a birnin Kaduna.

Ya taka rawa wajen shiga tsakanin tattaunawar ISWAP da gwamnatin Tarayya a baya wajen kubutar da fasinjojin jirgin kasa da aka sace a farkon shekarar nan.

A baya, ya taba shaidawa Muryar Amurka cewa ya janye daga shiga tsakani a kokarin kubutar da sauran fasinjojin saboda abin da ya kira barazana da rayuwarsa take fuskanta.

Wata majiyar tsaro ta tabbatar da aukuwar hakan inda ta bayyana cewa lalle kam Interpol ta kame dan jaridar a kasar Masar akan hanyarsa ta zuwa Saudiyya.

A baya hukumomin sun taba zargin Tukur Mamun da alaka da ‘yan bindigar amma kuma ya sha musanta wannan zargi.

XS
SM
MD
LG