Yayin da lamarin tsaro ke ci gaba da ta’azzara a wasu sassan Najeriya, rundunar mayakan ruwa na taka muhimmiyar rawa wajen ganin an samar da zaman lafiya a ciki da wajen kasa.
A ci gaba da samun nasara da sojojin Najeriya ke yi a baya bayan nan, dakarun Operation Hadarin Daji da ke aiki a arewa maso yammacin Najeriya, sun damke wasu miyagu da su ka shigo daga kasashen ketare.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce an sake damko karin wasu yan ta'adda guda biyu dake cikin maharan da suka kai harin cocin Owo
Shi dai wannan kwamanda na Boko Haram shi ne wanda a shekarar 2014 ya jagoranci kai farmakin da ya yi sanadin kashe daruruwan mutane a garin Bama tare da maida garin karkashin ikon abin da suka kira Daularsu
Kusan kashi saba'in cikin dari na mutanen da ake safara zuwa Jamhuriyar arewacin Cyprus ‘yan mata ne daga Najeriya kuma suna karewa ne cikin ayyuka da ke da alaka da nau'ikan bauta.
Hedkwatar tsaron Najeriya tayi watsi da zargin cewa sojoji na kitsa juyin mulki don hambarad da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Amurka da Burtaniyan sun fidda takardun gargadi ga yan kasashen nasu biyo bayan mummunan harin ta'addanci da aka kai gidan gyaran hali na koje dake yankin babban birnin Tarayyar Najeriya
Shugaban Najeriya ya kai ziyarar gani da ido gidan gyaran halin Kuje cikin wani farin jirgi mai saukar angulu, ya dudduba wuraren da 'yan ta'addan suka dagargaza.
Bayanai daga yankin tafkin Chadi na nuna cewa jiragen yakin rundunar dakarun kawancen kasashen yankin sun kaddamar da wani babban farmaki a kan ‘yan ta'addan kungiyar ISWAP inda suka hallaka da yawa daga cikinsu.
Shalkwatar tsaron Najeriya ta ce kimanin ‘yan Boko Haram dubu hudu da dari bakwai da saba’in ne suka ajiye makamansu tare da mika wuya ga sojoji a sassa dabam daban na arewa maso gabashin Najeriya a watan Yuni.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta bada umarnin korar wasu jami'ai daga rundunonin sojojin kasar da ya kunshi yin ritayar dole ga sojojin da basa da kyakkyawan hali na gari da aka samu da aikata ba daidai ba.
‘Yan bindiga sun kai hari a karamar hukumar Abaji inda suka yi awon gaba da manoma 22 a kauyen Rafin Daji da ke kan iyakar babban birnin tarayya Abuja da jihar Neja mai fama da matsalar tsaro.
Kalaman na babban hafsan tsaron rundunonin sojin Najriya na zuwa ne yayin da kasar ke fama da matsalar hare-haren Boko Haram da na 'yan bindiga masu garkuwa da mutane.
Rundunar Mayakan Amurka ta Horas da manyan kwamandojin sojojin Najeriyar da nufin lalubo karin hanyoyin da za ake kare fararen hular da ba suji ba basu gani ba yayin da sojoji ke fafatawa ko kuma wani aikin samar da zaman lafiya a sassan Najeriya.
A ci gaba da yaki da satar gurbataccen mai, gudanar da haramtattun matatun mai da ma fasa kwaurinsa shirin sintirin rundunar sojojin ruwan Najeriya mai suna OPERATION DAKATAR DA BARAWO ta yi nasarar hana Najeriya hasarar kusan Naira milyan dubu biyu.
Babban Hafsan Hafsoshin rundunar sojojin Najeriya Laftanar Janaral Faruk Yahaya ya ce ya ba da umarnin sake bitar irin rawar da sojoiji za su taka yayin gudanar da zabuka a Najeriya a shekara mai kamawa idan Allah ya kaimu.
Dakarun kawancen Tafkin Chadi na ci gaba da mamaye tsibiran dake zama tungar 'yan ta'addan ISWAP a bangarorin Najeriya da Chadi.
Bulaguro ta sama na daya daga cikin hanya mafi ingancin sufuri a Najeriya idan aka yi la’akari da matsalolin tsaro da ya mamaye hanyoyin mota a kasar.
Rundunar dakarun kawancen na yankin tafkin Tchadi tace mummunan farmakin aiki da cikawa da ta kaddamar mai take OPERATION LAKE SANITY, kimanin mayakan ISWAP da Boko Haram 800 ne ta hallaka.
Dakarun Najeriya da Chadi sun kai wani mummunan farmaki a tsibiran tafkin Chadi a ci gaba da fafatawar kawo karshen 'yan ta'adda.
Domin Kari