Yajin aikin da ‘yan kungiyar masu sana’ar tuka babur mai kafa uku da akafi sani da Adai-daita sahu ya gurgunta harkokin sufuri a birni da kewayen Kano.
Gwamnan Kano ya ce hakkin gwamnati ne ta samar da zaman lafiya a cikin al'umma. Hakan yasa gwamnatin Kano ta dauki mataki biyo bayan wasu kalamai na Sheikh AbdulJabar Nasiru Kabara.
Aikin rushe-rushen gine-gine da hukumar raya birane ta jihar Kano (KNUPDA) ta gudanar a ranar Asabar dinan a filin Mushe na unguwar Gwale a binrin Kano ya haifar da cece-kuce tsakanin ma’aikatar ilimi ta jihar Kano da al’umar yankin.
Jami’an tsaro a Kano sun yi kawanya a masallacin Ashabul Khafi dake Unguwar Gwale a cikin birnin Kano, wurin da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ke gudanar da karatu.
A Najeriya wata takaddama kan mallakar wuraren ibada a birnin da kewayen Kano na ci gaba da wakana tsakanin mahukuta a matakai daban daban da kuma kungiyoyi da cibiyoyin al’uma dana addinai a jihar Kano.
Makiyaya da masana dokokin kasa sun mayar da martani ga kiran gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje na samar da dokar da zata haramtawa Fulani makiyaya shiga yankin kudancin da sunan kiwo.
Gwamnatin Jihar Kano a Najeriya na shirye-shiryen samar Jami’an tabbatar da ganin cewa Jama’a na bin sharuddan kare kamuwa da cutar coronavirus, su kimanin dubu guda, wadanda ta yi wa lakabi da darakarun COVID.
An samu nasarar sako wasu da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su.
Zaben kananan hukumomi da ya wakana a jihar Kano a ranar Asabar ya fuskanci karancin jama’a da suka fita kada kuri'a, ko da yake rahotanni sun ce zaben ya wakana cikin lumana.
Ganin yadda takwarorinsu a kudu ke ta hada hadar kasuwanci sanadiyyar zirga zirgar jiragen sama a yankunansu, 'yan kasuwa a arewacin Najeriya da masu harkoki da jiragen sama na kiran da a bar jiragen kasashen ketare su rika sauka a Filin Jirgin Saman Kasa da Kasa Na Mallam Aminu Kano.
A wani mataki da masu ruwa da tsaki su ka ce na tabbatar da nasarar zaben Kananan Hukumomi ne da za a yi a Kano ranar Asabar, an shirya ma masu sa ido kan zaben taton bita.
Tsohon gwamnan Kano Sanata Ibrahim Shekarau ya ce rashin hadin kai tsakanin gwamnatocin arewa na taka mummunar rawa wajen tabarbarewar al’amura a yankin, yayin da kungiyoyin rajin shugabanci na gari ke kokawa kan yadda sukace shugabannin arewan ba sa sauraron shawarwarin su.
Ma'aikatan Jihar Kano sun koka dangane da matakin gwamnati na rage albashin da aka biya su a watan Disamba da ya gabata, yayin da su kuma 'yan fasho suka yi korafin rashin samun fansho na wata-wata.
Yayin da mazauna lardin arewacin Najeriya ke fama da kalubalen tsaro da tattalin arziki da kuma rashin ayyukan yi, an kafa wata sabuwar kungiya da nufin farfado da martabar yankin na Arewa.
Hukumar kula da hakkoki da karfafa gwiwar ‘yan kasa akan harkokin albarkatun mai da Iskar gas ta Najeriya ta ce damar da kamfanonin cikin gida masu hada-hada a bangaren albarkatun mai na kasar sun karu da kimanin kashi 30 cikin dari.
Yayin da ‘yan kungiyoyin gwagwarmayar shugabanci na gari a Najeriya ke caccakar matakan wasu gwamnonin arewacin Najeriya na rufe makarantunsu, dalibai a kwalejin nazarin ilimin aikin malinta ta Sa’adatu Rimi a Kano sun gudanar da zanga-zanga.
Hukumar da ke yaki da masa tu'ammali da ababen maye a Najeriya, ta ce ta samu daruruwan masu amfani da ababen maye a tsakanin 'yan takarar da ke neman mukamai a zaben kananan hukumomi da za a yi a karshen mako nan a jihar Kano.
Mazauna yankin arewacin Najeriya na bayyana halin kuncin rayuwa da fargaba da suke ciki saboda ci gaba da tabarbarewar yanayin tsaro a yankin. Sai dai masana da masu Nazari na sharhi akan dalilai da kuma hanyoyin bi domin magance matsalar.
Ziyarar wasu gwamnonin Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, na ci gaba da tada kura a fagen siyasar kasar.
Yayin da miyagu ke ta cin karensu ba babbaka a arewacin Najeriya mai fama da tsadar rayuwa, jama'ar yankin - kama daga masu fada a ji zuwa talakawa - na ta wayyo Allah.
Domin Kari