Hukumomi a jihar Kano sun ce tashar samar da lantarki mai zaman kanta da gwamnatin jihar ke ginawa a madatsar ruwan Tiga za ta fara aiki a zangon farko na shekarar 2021.
Duk da cewa a jihar Kano ba a samu zanga zangar ENDSARS ko tarzomar fasa runbunan gwamnati ba, amma akwai tarin korafi kan zargin cin zalin da wasu ‘yan sanda suka yi wa fararen hula.
An kaddamar da aikin gwajin cutar hawan jini a wasu cibiyoyi a jihohin Kano Da Ogun a Najeriya.
A cigaba da dauke hankali da dambarwar zaben Amurka ke kara yi, tsohon gwamnan jahar Jigawsa kuma tsohon Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Sule Lamido ya ce lallai wannan al'amari na tattare da abin koyi ga kasashe masu tasowa kan muhimmancin hadin kai.
Majalisar dokokin jihar Kano ta bayyana damuwa akan yadda harkar ilimi a jihar ta kama tafarkin tabarbarewa saboda karancin malamai a makarantun jihar.
Kungiyar malaman Jami’o’I a Najeriya wato ASUU na dakon gwamnatin tarayya ta fitar da sakamakon gwajin tabbatar da sahihancin sabuwar manhajar da kungiyar ta samar wadda jami’o’in zasu rinka amfani da ita wajen sarrafa kudaden gudanar da ayyukan su.
Yayin da matasa ke kai farmaki kan rumbunan adana kayan abinci na gwamnati a wasu jihohin Najeriya, gwamnatin Kano ta kafa kwamitocin kula da lamuran tsaro a kananan hukumomi, a daidai lokacin da dattawan arewa ke ci gaba da jan hankalin matasan game da illar tarzoma.
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA zata gudanar da gwajin ta’ammali da miyagun kwayoyi da ababen sanya maye akan dukkanin ‘yan takarar shugabancin karamar hukuma da kansiloli a kananan hukumomin jihar Kano 44
Yayin da aka shiga mako na biyu matasa na zanga zanga a Najeriya domin nuna damuwar su dangane da yadda ‘yan sanda ke gudanar da ayyukan su da kuma lamura masu nasaba da rashin tsaro, kwararru na ci gaba da bayyana hanyoyin da ya kamata a magance matsalolin da masu zanga zangar ke magana akai.
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana gudurinta na fitar da kudi Naira Miliyan dubu biyu da dari uku domin gudanar da zaben Kananan Hukumonin 44.
Yayin da batun inganta wasu manyan hanyoyin a arewa maso yammacin Najeriya ke samun jinkiri, gwamnatin Kano na duba yiwuwar gudanar da aikin tare da sauran gwamnatoci, daga baya gwamnatin tarayya ta biya su.
Yau litinin daliban makarantun firamare da na sakandare a jihar Kano ke komawa ajujuwa domin fara daukar darasi bayan shafe fiye da watanni bakwai a gida sandiyya annobar Corona.
Bayanai na nuna cewa rashin cancantar daliban jahar Kano ta Najeriya ya haifar da tafiyar hawainiya ga kwalejin gamayya ta Jamhuriyar Nijar da jahar Kano ta Najeriya.
Fiye da wata guda bayan babban bankin Najeriya CBN ya amince da fara aiki da tsarin bada lamanin da babu ruwa ga kananan da matsakaitan ‘yan kasuwa da sana’o’I, masu kula da lamura a wannan fanni na ci gaba da bayyana matakan da suka kamata a dauka da zai farfado da harkokin kasuwanci a kasar
Takaddamar da ta biyo bayan hukuncin da wata kotun Shari'ar Musulunci ta yanke ma wasu matasa a Kano na cigaba da aukuwa, ganin yadda hukumar Asusun Yara Ta Duniya (UNICEF) ta shigo, malamai kuma ke cigaba da bayani.
Yajin aikin 'yan kungiyar likitocin masu neman kwarewa a Najeriya ya kara jefa miliyoyin marasa lafiya cikin halin kaka na kayi a kasar.
Yahaya Aminu Sharif, matashin nan dan shekaru 22 da kotun shari’ar Musulunci ta jihar Kano ta yankewa hukumcin kisa ya daukaka kara ‘yan kwanaki kafin cikar wa’adin kwana 30 da kotu ta bashi na daukaka kara.
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano tana tuhumar mutumin da ya daure dan sa a gida ba tare da cikakkiyar kulawar ciyarwa da ta kiwon lafiya ba na tsawon shekaru bakwai.
Yayin da kotun shari'a Musulunci a jihar Kano ta yanke hukuncin kısa ga wasu mutum biyu cikin wannan makon, lamarin ya ta da kura a sassan jihar.
Babbar kotun shari’ar musulunci a jihar Kano ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani matashi dan shekaru 22.
Domin Kari