Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban riko na kasa a jam’iyyar APC mai mulki, Mai Mala Buni, shine ya jorancin tawagar gwamnonin jam’iyyar APC zuwa Bayelsa, da sunan taya tsohon shugaba Goodluck Jonathan murnar cika shekaru 63 da haihuwa.
Tuni dai jam’iyyar PDP mai hamayya ta Jonathan, ke cewa ziyarar wata manuniya ce dake tabbatar da cewa, gwamnatin PDP ta kwatanta adalci cikin shekaru 16 na mulkin ta.
Tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, na kallon wannan ziyara ta gwamnonin tamkar sun kaiwa jam’iyyar PDP ne, ganin yadda lokacin mulkin Jonathan babu abin da ba a fada masa ba na batanci.
Duk da cewa, gwamnonin sun ce taya murna ga tsohon shugaban shine makasudun ziyarar, amma manazarta na fassara ta da cewa alamu ne dake nuna APC na zawarcin shugaba Jonathan.
Lamarin da Sanata Masa'ud El-Jibril Doguwa, dake zaman mamba a Jam’iyyar ta APC ke cewa idan hakan gaskiya ne to akwai gyara. Domin daga lokacin da jam’iyya mai mulki ta fara zagayawa neman ‘yan adawa da suke taimakawa don tabbatar da dimokaradiyya, to lamari ya fara lalacewa.
Saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.