Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kano Ta Musanta Rusa Makarantar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara


Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje

Aikin rushe-rushen gine-gine da hukumar raya birane ta jihar Kano (KNUPDA) ta gudanar a ranar Asabar dinan a filin Mushe na unguwar Gwale a binrin Kano ya haifar da cece-kuce tsakanin ma’aikatar ilimi ta jihar Kano da al’umar yankin.

Sabanin yadda wasu kafofin labarai a Najeriya suka wallafa rahotanni, rushe -rushen bai shafi makaranta mallakar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ba, mutumin da gwamnatin jihar Kano ta yiwa daurin talala a gidan sa tun daga ranar Alhamis din nan.

Sai dai majiyoyi daga unguwar sun tabbara da cewa, shehin malamin na amfani da wani bangare na filin da gine-gine basu kai gareshi ba wajen gudanar da wa’azin sa a lokuta daban-daban.

A nata bangare, hukumar raya birane ta jihar Kano ta musanta cewa ta rusa makarantar Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara, a cewar kakakin hukumar Ado Mohammed Gama.

Tun a shekara 2002 ne gwamnatin jihar Kano ta yanka fulotai a filin wadda gabanin haka tsohuwar makabarta ce da ake bunne mutane.

Bayan samar da Fulotan gwamnati ta mallaka su ga wasu daga cikin mazauna unguwar ta Gwale da sauran makwafta. Amma a wancan lokaci mutane ba su fara ginawa ba saboda tsoron tuno gawawwaki.

Malam Rabiu Gwale dake zaman sakataren kungiyar ci gaban Gwale ya ce wadanda aka mallakawa fulotan sun fara gine-gine a karshen shekara 2020, wato bara kenan.

Sai dai a cikin watan jiya na Janairu ma’aikatar ilimi ta ce, zatayi amfani da filin domin gina makaranta saboda ta gano wata wasika da wasu mutane suka aika mata tun shekarun baya suna muradin a gina makarantar a wurin, saboda gwamnatin Kano ta soke fulotan data tsara a wurin tun a shekara ta 2012, kamar yadda kwamishinan ilimi na jihar Alhaji Muhammad Sanusi Kiru ke cewa.

To amma sakataren kungiyar ci gaban Unguwar ta Gwale Malam Rabiu ya ce ba san da wannan magana ba, yana mai cewa, kafin su fara gine-ginen su sai da suka sanar da ma’aikatar dake kula da taswirar bini da kewayen Kano wadda itace ta fitar musu da taswirar yadda gine-gine a wurin zasu kasance, tare da bada lambar fuloti ga mutane da aka baiwa.

A don haka sai Malam Rabiu, ya ce suna rokon gwamnati ta ja hankalin ma’aikatar ilimi game da wannan batu, la’akari da cewa, galibin fulotan da gine-ginen da aka fara mallakar Marayu ne a yanzu.

XS
SM
MD
LG