Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnatin tarayya ta sanya Kano a rukunin farko na jihohin da za su fara amfani da allurar rigakafin cutar ta Corona a cikinsu, bayan karkare tattauanawa tsakanin gwamnatin da kamfanonin da suka samar da rigakafin.
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, wanda ke neman hadin kan masu ruwa da tsaki kan matakan da gwamnatinsa ke bi na dakile cutar ta Corona ya ce dakarun na COVID za su samu tallafi daga jami’an tsaro na ‘yan sanda da sauran jami’ai da ke sanye da kayan sarki.
Ya ce “Zamu fito da dakarun korar COVID, matasa da suka kai kaman dubu daya da zasu taimaka wurin fadakar da mutane musamman a kan muhimmancin saka takunkumin hanci da baki.”
Dr. Tijjani Hussaini da ke zaman Kodinatan ayyukan yaki da cutar Corona a Jihar Kano, ya yi karin haske dangane da batun sinadaran allurar rigakafin Corona da Kano ke dako.
Ya ce gwamnati ta dauki matakai daban daban, musamman gwamnatin tarayya, wacce take kokarin tabbatar da sahihancin allurar rigakafin da za a kawo a Najeriya. Ya ce a mataki na jiha kuma za su wayar da mutane cewa allurar ba ta da illa.
Alkaluma daga sakatariyar kwamitin yaki da Corona ta jihar Kano, sun nuna cewa, tun farkon shigowar cutar Coronar jihar a bara, ya zuwa juma’ar makon jiya, jimlar mutane 63,362 aka yi wa gwaji a jihar, amma sakamakon gwajin ya tabbatar da ita a kan mutane 2,730, yayin da tayi sanadin mutuwar mutane 70
Daga Kano ga rahotan da Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko mana: