Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shawarar Ganduje Kan Makiyaya Ta Saba Doka-Bulama Bukarti


Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje

Makiyaya da masana dokokin kasa sun mayar da martani ga kiran gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje na samar da dokar da zata haramtawa Fulani makiyaya shiga yankin kudancin da sunan kiwo.

Dayake amsa tambayoyin manamen labarai a karshen makon jiya a garin Daura na jihar Katsina dake arewa maso yammacin Najeriya, gwamnan na Kano ya ambata cewa, ya kamata gwamnatin tarayya ta samar da wata doka ta bai daya da zata hana Fulanin arewa zuwa yankin Kudancin Najeriya domin gudanar da harkokin kiwo a can.

Hakan a cewar gwamnan, zai kawo karshen fitinar dake wakana tsakanin makiyayan da manoma, baya ga magance matsalar satar shanu da akan yiwa makiyayan daga lokaci zuwa lokaci.

Shanun Fulani Makiyaya
Shanun Fulani Makiyaya

Da yake maida martani kan shawarar gwamnan a zantawa da Muryar Amurka, kakakin kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah a yankin Tsanyawa dake arewa maso yammacin Kano, Moddibo Ado Maikwalta, ya ce, wannan ba shine karon farko da gwamna Ganduje ya yi makamantan wadannan kalamai ba.

“Mai girma gwamna ya taba Magana makamanciyar wannan lokacin da aka sami hatsaniya tsakanin makiyaya da manoma a wasu sassan kasar, yake cewa, duk makiyayin daya rasa wurin kiwo ya zo jihar Kano, kuma makiyaya sun amsa wannan kira. Yanzu haka akwai garken shanu fiye da dubu biyar a yankin Tsanyawa kawai, amma matsalar da muke fuskanta itace daga wancan lokaci kuma manoma suka maida hankalin su wajen nome Burtala da makiyayu, ka ga kenan akwai matsala domin wurin da muke kiwon dabbobin mu ana ta nomewa”

Taron Kungiyar Makiyaya a Kaduna 2
Taron Kungiyar Makiyaya a Kaduna 2

Kakakin kungiyar ta Miyetti Allah ya kara da cewa, a hannu guda kuma, su kuma bakin Fulanin na tunkaho cewa, gwamna ne ya gayyato su domin haka kada a tsangwame su. Yace lamarin ya jefa su cikin tsaka mai wuya a yankin.

A nasa bangaren, Audu Bulama Bukarti, Lauya mai zaman kansa a Najeriya dake karatun Digirin Digirgir a London, yace dokar da gwamnan na Kano ke kira a samar da ita ta ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ya bayyana cewa, “Kundin tsarin Mulki yace ba za’a iya hana duk wani dan Najeriya tashi daga wani bangare zuwa wani ba sai da dalilai guda uku, ko dai ya kasance ya aikata wani laifi aka kama shi aka kulle a kurkuku, ko kuma ana zargin sa da laifin ya ki zuwa kotu. Dalili na biyu, idan yana dauke da wata cuta mai yaduwa kamar CORONA VIRUS, idan aka bar shi zai yada ta daga arewa zuwa kudu ko daga kudu zuwa arewa to sai a hana shi zuwa. Dalili na uku kuwa shine, idan yaro ne dan kasa da shekara 18, ana so a ilimantar dashi a makaranta, za’a iya hana shi zuwa wani wuri domin a ilimantar dashi. Shawarar da gwamna Ganduje ya bayar ba ta daya daga cikin wadannan abubuwa guda uku kuma kundin tsarin mulkin Najeriya yace haramu ne ayi wata doka data ci karo da kundin tsarin mulkin”

Barrister Bulama ya kara da cewa, kundin tsarin Mulki bai san kudu ko arewa a yanayin zamantakewar Najeriya ba.

Kusan shekara guda kenan gwamnantin jihar Kano ta kaddamar da shirin gina Ruga ga Fulani makiyaya, wadda a karkashin sa, zata samar da filayen kiwo, samar da ruwa ga dabbobi, makarantu domin ‘yayan makiyaya da sauran muhimman abubuwan da makiyayan ke bukata. Sai dai ga alama shirin bai fara tasiri ba tukunna.

Saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00


XS
SM
MD
LG