Da tsakar daren ranar Talata 15 ga watan Disamba ne gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bada umurnin rufe daukacin makarantun da ke jihar.
Ga alama matakin gwamnan bai yi wa iyaye da yawa dadi ba musamman da ya ke gwamnati ba ta bayyana musu dalilin rufe makarantun ba.
Yayin da iyaye ke bayyana damuwarsu dangane da sake rufe makarantu a jihar ta Kano, su kuwa daliban kwalejin nazarin ilimin aikin malinta ta Sa’adatu Rimi mallakar gwamnatin jihar, zanga-zanga su ka gudanar a ranar 16 ga watan Disamba ta nuna rashin jin dadinsu akan matakin.
Sai dai jami’an tsaro sun yi nasarar daidaita al’amura cikin sa’o’i kalilan,daga bisani shugaban kwalejin Dr. Yahya Isa Bunkure, ya bayyana dalilan rufe makarantun a Kano, inda ya ce rufe makarantun na da nasaba da kalubalen tsaro a arewacin kasar, duba da irin abinda ya faru a garin Kankara da ke jihar Katsina.
Sai dai masu kula da lamura na yau da kullum na cewa gurguwar dabara ce gwamnonin ke yi. Kwamred Kabiru Sa’idu Dakata, dan gwagwarmayar tabbatar da shugabanci na gari ne a Najeriya, ya ce kamata ya yi a bi hanyoyin da za a bai wa makarantu kariya. Ya kara da cewa hanya daya ya kamata gwamnatoci su bi, ita ce magance matsalar tsaro a kasar.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ke sasantawa da kungiyar malaman Jami’o’in kasar akan yajin aikin da suka shafe watanni tara su na yi.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari: