A yayin wani taron karawa juna sani na ma’aikatan kafofin labarai da aka yi a Kano, daraktan ayyukan dokoki da shari’a na hukumar Barista Mohammed Babangida Umar, ya ce zuwan hukumar ya kawo sauye-sauye a sha’anin tafiyar da bangaren mai da iskar gas a Najeriya, shekaru goma bayan kafuwarta, duk kuwa da kalubalen da ta ke fuskanta.
Alhaji Abdulmalik Halilu, da ke zaman babban manajan kula da harkokin bincike da kididdigar alkaluma a hukumar, ya yi tsokaci game da nasarorin da suka samu wajen zartar da dokokin da suka kafa hukumar, ya ce sun canza tsarin ta yadda 'yan Najeriya ne zasu samu ayyukan da suka shafi hakar rijiyar mai, yanzu mutane da yawa sun saka jari a gina masana'antu da zasu kawo kayayyakin aikin, abinda ya kara samar da ayyuka ga matasa da kuma hanyoyin samun kudin shiga ga gwamnatin kasar.
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda Dangorubar Kano Alhaji Abubakar Sule Gaya ya wakilta, ya nanata bukatar da ke akwai ga masu ruwa da tsaki a bangaren albarkatun mai da iskar gas su dafa wa ayyukan hukumar alfanun ‘yan kasa.
Batun aikin shimfida bututun iskar gas daga Ajakuta zuwa Kano na daga cikin aikace-aikacen da wannan hukuma ta kula da hakki da karfafa gwiwar ‘yan kasa akan harkokin albarkatun mai da Iskar gas ta Najeriya, wato Nigerian Content Development & Monitoring Board, ke sanya ido akai domin ganin an dama da kamfanonin cikin gida.
Saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.