Batun biyan harajin naira 100 ga gwamnati kuma a dunkule na tsawon shekara guda shine musabbabin takaddamar da ta kaure tsakanin matuka adai-daita sahun da kuma hukumar KARATO mai kula da zirga zirgar ababen hawa wadda tun a makon jiya aka fara kai ruwa rana tsakanin jami’anta da matuka baburan mai kafa uku.
Wannan lamari dai ya kawo cikas ga zirga zirgar Jama’a a birnin da kewayen Kano a yau litinin musamman ga ma’aikata, dalibai da kuma ‘yan kasuwa.
Ya zuwa yanzu dai Uwar kungiyar matuka baburan na adai-daita sahu a Kano ta nesanta kanta da wannan yajin aiki da ‘yayan ta keyi.
Ga alama wannan takaddama ta sanya hukumar KAROTA mai kula da zirga zirgar Ababen hawa a Kano baiwa gwamnatin shawarar rusa tsarin sufurin adai-daita sahu a jihar Kano, kamar yadda shugabanta Babbafa Babba DanAgundi ya tabbatar.
Gwamnatin Kano ta Malam Ibrahim Shekarau ce ta bullo da tsarin sufuri na adai-daita sahu kuma Dr Saidu Ahamad Dukawa na cikin wadanda suka bada gudunmawar samar da tsarin a wancan lokaci.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari cikin sauti: