Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sai Gwamnatocin Arewa Sun Hada Kai Kafin Kai Ga Nasara-Shekarau


Shekarau
Shekarau

Tsohon gwamnan Kano Sanata Ibrahim Shekarau ya ce rashin hadin kai tsakanin gwamnatocin arewa na taka mummunar rawa wajen tabarbarewar al’amura a yankin, yayin da kungiyoyin rajin shugabanci na gari ke kokawa kan yadda sukace shugabannin arewan ba sa sauraron shawarwarin su.

Sanata Ibrahim Shekarau wanda ke Magana da manema labarai a Kano a karshen mako ya ce matsalolin arewa na bukatar hada karfi da karfe tsakanin masu ruwa da tsaki kafin a kai ga magance su.

Ya ce mutane kan yi misali da irin rawar gani da magabata kamar su Sardauna suka taka wurin ci gaban yankin arewacin Najeriya. Sanata Shekarau ya kara da cewa a wancan zamani Sardauna kadai ke aiki a fadin arewacin Najeriya a matsayinsa na gwamnan Arewa, to amma yanzu Arewa nada gwamnoni 19 kuma kowa na zaman kansa, dan haka zai yi wahala a samu yadda ake so.

Sai dai Dr Dalhatu Sani Yola na kungiyar farfado da martabar arewa ta Northern Reform Organization wato NRO a takaice na cewa, kodayake akwai kungiyar gwamnonin arewa da sauran kungiyoyi da gwamnononin ke tattaunawa atsakaninsu, amma akwai bukatar mutanen arewan su farga ta hanyar tofa albarkacin bakinsu kan matsalolin da suka dabaibaye rayuwarsu.

Ya ce babban abin da arewacin Najeriya shine mutane da basu magana kuma rashin masu magana na taimakawa wurin matsaloli da yankin ke huskanta. Ya ce mutanen kudancin kasar dake magana game da ayyukan shugabanni, yasa ana basu kulawan da ya dace har ma shugaban kasa kan tura mutane idan an kashe koda mutum guda a kudu amma ba haka batun yake ba a arewa.

To amma kungiyoyin rajin shugabanci nagari a yankin na arewa na ganin gwamnanonin ne da sauran shugabannin gwamnati a Najeriya ba su sauraro tare da aikin da shawarwarin da ake basu.

Kwamrad Abdulrazak Alkali jigo a gamayyar kungiyoyin fararen hula da dake rajin shugabanci na gari a Najeriya ya tattauna da Muryar Amurka a kan wannan zargin, inda ya ce sau tari suna zama da shugabannin kuma suna basu shawarwari a kan batutuwa da suka shafin sha’anin mulki amma kuma sai su yi watsi da abubuwan da suka tattauna akai.

Ya ce an neme su wurin wani taron koli a kan tsaro a jihar Kano wanda ministoci Kano guda biyu suka gudanar amma kuma ya ce ba a bawa jama’a dama sun bayyana ra’ayoyin su ba wanda ta hakan ne za a samu hanyar warware matsaloli.

Daga Kano ga rahotan Mahmud Ibrahim Kwari:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG