‘Yan kasuwa a yankin arewacin Najeriya sun kalubalanci gwamnatin kasar da sauran masu ruwa da tsaki a fannin zirga zirgar jiragen sama akan ci gaba da haramta wa kamfanonin jiragen sama na ketare sauka da tashi a filin jirgin saman Malam Aminu Kano, da ke Kano.
Tun a watan Maris na bara ne gwamnatin Najeriya, ta hannun ma’aikatar kula da sufurin jiragen sama ta kasar ta dakatar da jiragen ketare sauka da tashi a filin jirgin saman na Kano, biyo bayan barkewar cutar Korona.
Kodayake wannan mataki ya shafi sauran tasoshin jiragen sama na kasar, amma bayan daidaitar lamura, gwamnati ta sake bude filayen jiragen sama na Lagos, Abuja da kuma Fatakol, yayin da na Kano ke ci gaba da zama a rufe.
Alhaji Muhammadu Sanusi Wakili, shugaban kungiyar kamfanin dake auna kayakin da ake safararsu ta jiragen sama ta Najeriya reshen tashar jirgi ta Malam Aminu Kano, ya jaddada wannan matsayin da kuma bayyana damuwa kan tasirin hakan.
Baya ga haka, su ma kamfanonin dake aikace aikacen fiton kayayyaki a tashar jiragen saman ta Aminu Kano na kokawa, Alhaji Abdulrashid Nasidi, shugaban kungiyarsu ya ce al’amarin na matukar masu illa.
Sai dai Alhaji Muhammadu Sanusi Wakili na cikin wadanda ke danganta wannan matsala da halin ko in kula da shugabannin arewa a matakai daban daban ke nunawa ga tashar jirgin ta Kano, duk da muhimmancin Kano da arewa baki daya a fagen kasuwancin kasa da kasa.
Masu kula da lamura dai na ganin samar da yanayin gudanar da hada hada yadda ya kamata a tashar jirgin saman ta Kano ka iya taimakawa wajen karfafa tattalin arzikin lardin arewa da ma kasar baki daya.
Ga Mahmud Ibrahim Kwari da cikakken rahoton: