Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Kano


Zaben kananan hukumomi da ya wakana a jihar Kano a ranar Asabar ya fuskanci karancin jama’a da suka fita kada kuri'a, ko da yake rahotanni sun ce zaben ya wakana cikin lumana.

Baya ga rashin fitowar jama’a a zaben, an kuma fuskanci jinkirin isar kayayyaki zuwa tashoshin zabe a sassa dabam-daban na jihar duk da tanadin samar da kayan akan kari da hukumar zabe ta jihar ta yi.

Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kano, Murtala Sule Garo, ya ce babu wata matsala da aka fuskanta a zaben illa matsalolin rashin kai kayan aiki akan lokaci.

Ya zuwa yanzu dai akwai mabambantan ra’ayoyi game da dalilan da suka sa galibin al’umar jihar suka kaurace wa zaben.

Honarabul Sha’aban Ibrahim Sharada, mai wakiltar karamar hukumar Birnin Kano a majalisar wakilan Najeriya kuma dan jam’iyyar APC, ya ce masu goyon bayan jam'iyyarsu da ke yi musu hidima, sun sayi fom a karamar hukumar Birni, mutane shugabannin jama'iyyu kashi 85 cikin 100 suka ce zasu zabi 'yan bangarensu, amma ana ji ana gani karfi da yaji aka ce ba su isa ba.

Wani kalubale da zaben na jiya ya fuskanta shi ne yadda aka rinka watsa hotunan yara akan layi a kafofin sada zumunta, ana cewa suna cikin masu kada kuri’a.

Farfesa Garba Ibrahim Sheka, da ke zaman shugaban hukumar zaben jihar ya ce dama ba za a rasa masu yin sharri a zaben ba, ya kuma karyata zargin hotunan kananan yaran da aka ce sun yi zabe.

Duk da kalubalen da zaben na jiya ya fuskanta, Honarabul Garba Unguwar Rimi na cikin jami’an gwamnatin Kano da ke alfaharin wakanar sa cikin lumana, ya na mai cewa an yi zabe lafiya ba tare da tashin hankali ba kuma ya yaba wa kafafen yada labarai da suka goya musu baya game da wannan zabe.

Yanzu haka dai masu kula da al’amura a harkokin zaben kananan hukumomi a Najeriya na bayyana matakan bi domin farfado da kimar zabe a idanun ‘yan Najeriya.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, jam’iyya mai mulki ta APC ce ta yi nasarar samun kujeru fiye da 30, kana rahotanni sun inganta cewa dama jam’iyyun hamayya ba su yi wani tasiri ba a kananan hukumomi 44 da mazabun kansiloli 484 da ke fadin jihar ta Kano.

Saurari karin bayani cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Karin bayani akan: APC​, Jihar Kano, Nigeria, da Najeriya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG