Batun kalubalen tsaro da tsadar rayuwa da kuma tabarbarewar tattalin arziki, na ci gaba da yin mummunan tasiri kan ‘yan Najeriya, musamman mazauna yankin arewacin kasar. Yanzu haka dai dattawa a yankin arewa da sauran masu ruwa da tsaki na bayyana matakan bi domin lalubo mafita.
Al’amarin baya bayan nan, shi ne yadda batagari ke satar mutane domin karbar kudin fansa akan hanyar Kaduna zuwa Abuja, baya ga farmarkin da tsageru ke kaiwa Kauyuka da garuruwa a jihohin Kastina, Zamfara da Sokoto da dai sauransu.
Yanzu haka dai masu sharhi na ci gaba da jan hankalin mahukunta kan bukatar karkata hankulansu game da halin da lardin na arewa ke ci. Honorabul Nasiru Garba Dantiye tsohon wakili a zauren Majalisar Dokokin Najeriya, na daya daga cikin wadanda ke bayyana damuwarsu kan wannan al'amarin.
To amma Dattijo Abdulkarim Dayyabu da ke zaman 'kwamandan' Rundunar Tabbatar Da Adalci a kasar, na cewa, Shugaban Ma’aikata a Fadar Gwamnatin Tarayya shi ke da muhimmiyar rawar takawa wajen daidaita tafiyar gwamnatin Najeriya.
Sai dai shugabannin siyasa irin su tsohon gwamnan Jigawa, Alhaji Sule Lamido na ganin lokaci ya yi da ya kamata jagorori, musamman ma a lardin na arewa, su fada wa juna gaskiya da nufin daidaita lamura.
Ga Mahmud Ibrahim Kwari da cikakken rahoton: