Kimanin shekara guda kenan wasu daga cikin gwamnatocin jihohin Najeriya suka bi sahun gwamnatin kasar na fara amfani da sabon mafi karancin albashi na Naira 30,000 ga ma’aikatan gwamnati.
Jihar Kano dai na daya daga cikin jihohin da suka fara aiwatar da wannan tsari bayan gwagwarmaya da shugaban kungiyar kwadagon Najeriya.
Sai dai watanni kalilan bayan fara amfani da wannan sabon tsari, sai kwatsam a watannin Yuli da Agustan bara ma’aikata a jihar Kano suka wayi gari da samun albashi bisa tsohon tsari na Naira 18,000, lamarin da ya haifar da cece-ku-ce tsakanin gwamnati da ‘yan kwadagon jihar.
Ko da yake an sasanta da juna a wancan lokaci, amma samun gibin albashi a Kano ya ci gaba da wakana a watannin Nuwamba da Disambar bara.
Alhaji Shehu NaAllah, da ke zaman kwamishinan kudi a jihar Kano, ya ce annobar coronavirus ta kawo sauyi a fannin tattalin arzikin kasa, lamarin da ya sa bada albashin Naira 3,600 ba zai yiwu ba a jihar Kano, dole ne gwamnati ta yi amfani da abinda ke hannuta.
To sai dai Comrade Mansur Datti, masani kan dokokin kwadago da kwantarakin aiki na cewa albashi ba alfarma ba ne, wato bisa ga kundin tsarin mulkin Najeriya hakki ne na ma’aikaci don haka kuskure ne gwamnati ta ce ma’aikaci ya wayi gari bai san kan irin tsarin albashin da ya ke ba.
Baya ga ma’aikata su ma ‘yan fansho a jihar ta Kano sun fuskanci kalubalen rashin biyan alawus din fansho akan kari a watannin Nuwamba da Disamba na bara.
Saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari: