A watan Mayu ne ya kamata a fara jigilar danyen man Nijar daga tashar jirgin ruwan Seme a jamhuriyar Benin zuwa kasuwannin duniya, gwamnatin shugaba Patrice Talon ta yanke shawarar hana gudanar da wadannan ayyuka da nufin maida martani ga mahukuntan Nijar da ke ci gaba da rufe iyakar kasar.
Rukunin sojojin Rasha na biyu ya isa jamhuriyar Nijer wadanda aka ayyana a matsayin masu aikin horo a ci gaba da karfafa huldar aiyukan soja a tsakanin kasashen biyu bayan juyin mulkin da ya hambarar da shugaba Mohamed Bazoum.
A yayin da kasashen duniya ke bukukuwan karrama ranar ‘yancin aikin jarida a yau 3 ga watan Mayu, rahotanni na nuni da cewa ‘yancin aikin jarida da ‘yancin fadin albarkacin baki na fuskantar barazana a kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso.
Jami’an Amurka sun fara tantaunawa da shugabanin Majalissar CNSP mai mulkin Nijar da nufin tsara aiyukan ficewar dakarun Amurka 1,100 da ke girke a jihar Agadez yau shekaru sama da 10 a wani bangare na karfafa matakan yaki da ta’addanci a yankin Sahel.
An cimma wata yarjejeniyar da a karkashinta jamhuriyar Nijar ta amince ta sayar wa kasar Mali lita million 150 na man diesel akan farashi mai sauki.
Gwamnatin rikon kwaryar jamhuriyar Nijar ta sanar da karbar bashin dalar Amurka million 400 daga kamfanin man fetur CNPC na kasar China, domin daukan dawainiyar wasu daga cikin mahimman ayyukan kasa.
A jamhuriyar Nijar kungiyoyin kare hakkin ‘yan jarida sun bayyana damuwa bayan da jami’an tsaron jandarma suka kama wani dan jarida, Ousman Toudou, mai rajin kare dimokradiya kuma mashawarcin tsofaffin shugabanin kasa Issouhou Mahamadou da Bazoum Mohamed.
Gwamnatin rikon kwaryar jamhuriyar Nijar ta sanar da isowar wasu makamai da na’urorin kare sararin samaniyar da tace sun shigo ne albarkacin huldar ayyukan sojan dake tsakanin Nijar din da Russia.
Wata kotun birnin Yamai ta yi zama a yau juma’a 5 ga watan Afrilu ta 2024 da nufin nazari akan bukatar cire wa hambararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum, rigar kariya a wani yunkurin gurfanar da shi a gaban koliya a bisa zargin cin amanar kasa.
Matasa masu da’awar bunkasa dimokradiya da siyasar ci gaban kasa a jamhuriyar Nijar sun gargadi hukumomin mulkin soja akan bukatar fara shirye-shiryen mayar da kasar kan tafarkin dimokradiya kamar yadda suka yi alkwali a washegarin juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.
Wata kotun birnin Yamai ta umurci hukumomin jamhuriyar Nijar su gaggauta sakin wasu makusantan hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum daga inda ake tsare da su.
A yayin da Kiristoci a fadin duniya baki daya ke fara shirnin gudanar da bukukuwan Istan wannan shekar, fastoci na bayyana muhimmancin Good Friday kamar yadda Bishara mai tsarki ta nuna.
Sama da mako guda bayan da hukumomin jamhuriyar Nijar suka bada sanarwar yanke huldar ayyukan soja da Amurka gwamnatin Amurkar ta ce ta yi na’am da wannan mataki saboda haka nan gaba kadan kasashen biyu zasu tattauna kan hanyoyi mafi amfani wajen kwashe sojojin Amurkan daga kasar.
Wani harin kwanton bauna da aka kai a yammacin Laraba a yankin Tilabery kusa da iyakar Jamhuriyar Nijar da kasashen Mali da Burkina Faso ya yi sanadin rasuwar dakarun kasar sama da 20 wasu 17 suka jikkata.
A ci gaba da kwan gaba kwan baya da huldar Jamhuriyar Nijar da wasu kasashen Yamma ke yi, kasar da ke karkashin mulkin soji, ta yi shelar yanke huldar soji da Amurka.
Wata tawagar manyan jami’an gwamnatin Amurka da ke ziyara a jamhuriyar Nijar na ci gaba da tattaunawa da hukumomin rikon kwayar kasar a wuni na uku domin jin inda aka kwana game da tsare-tsaren jadawalin gudanar da al’amuran mulkin rikon kwarya.
Hukumomin mulkin sojan jamhuriyar Nijar sun soke harajin kayayyakin da aka yi oda domin amfanin jami’an tsaro da na fadar Shugaban Kasa da na gidaen manyan jami’an gwamnati da wadanda suka shafi tallafin ‘yan gudun hijirar cikin gida.
Domin Kari