Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hari A Mahakar Zinare A Nijar Ya Hallaka 'Yan Kasashe Da Dama


Mahaka
Mahaka

Wani harin sama da sojin Mali suka kai a wata mahakar zinare kusa da kauyen Tinzaouatene dake iyaka da Aljeriya ya rutsa da wasu ‘yan Nijar, da ‘yan Najeriya da kuma ‘yan kasar Chadi.

Lamarin dai ya haddasa asarar rayukan mutanen da kawo yanzu ba a tantance adadinsu ba, yayinda wadanda suka tsira suka shiga kiraye-kirayen ganin hukumomi sun gaggauta daukan matakan mayar da su gida.

Sanarwar da rundunar mayakan kasar Mali wato FAMA ta bayar a kafar talabijin mallakar gwamnati ORTM na cewa dakarun tsaron kasar da takwarorinsu na Burkina Faso a karkashin yarjejeniyar dake tsakanin kasashen AES sun kaddamar da ayyukan kakkaba na hadin guiwa a jiya Talata 30 ga watan Yulin 2024 ta hanyar amfani da jiragen sama a kewayen kauyen Tinzaouatene da zummar kare al’ummomi da dukiyoyinsu daga ta’asar da hadakar kungiyoyin ta’addancin ke tafkawa kan ‘yan kasar Mali.

Matakin ya bada damar wargaza ma’ajiyar makamai da sauran kayayyaki da lalata motoci da dama, saboda haka rundunar FAMA ta bukaci jama’a su kaurace wa wuraren da ‘yan ta’adda suka kafa sansani inji wannan sanarwa.

Tinzaouatene dake kusa da iyakar Mali da Aljeriya ne wasu sojojin Mali da ‘yan rakiyarsu na kamfanin Wagner suka rasu a ranar Lahadi 28 ga watan Yuli a yayin wani kazamin fadan da suka kwafsa da ‘yan awaren kungiyar CSP na arewacin Mali.

Mafari kenan hukumomin kasar suka tura jirage da nufin shan fansa kamar yadda wani mazaunin yankin da bai so a ambaci sunansa ya bayyana ta wayar tarho.

Yace bayan fadan ya kammala a ranar Lahadi ganin yadda kura ta lafa ‘yan kasuwa da masu ayyukan hakar zinare suka koma harakokinsu a mahakar ta Tinzaouatene, sai kwatsam a jiya da yamma jirgi maras matuki ya fara shawagi a take ya shiga barin wuta kan mutanen da ke nan da sauran wadanda ke shirin tserewa a motoci.

Wadanda muka zanta da su kuma sun bukaci hukumomi akan bukatar aike masu dauki.

Wata majiya a ma’aikatar harakokin wajen jamhuriyar Nijar ta bayyana cewa hukumomi na bin diddigin lamarin saboda haka ne ma aka umurci ‘yan kasar su dakatar da kai kawo a yankin sannan an bukaci su taru a wani wuri na musamman da aka kebe kafin nan gaba a fara kwashe su zuwa gida.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Wani Harin Sama Da Mali Ta Kai Mahakar Zinaren Tinzaouatene A Nijar Ya Hallaka 'Yan Kasashe Da Dama
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG