Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Zaman Makokin Kwana Uku A Nijar Bayan Harin 'Yan Bindiga Ya Hallaka Sojoji 20


'Yan bindiga
'Yan bindiga

Gwamnatin Nijar ta ayyana zaman makokin kwanaki uku daga yau Laraba bayan rasuwar sojojinta 20 da farar hula 1 lokacin wani harin ta’addanci da ya rutsa da su a kauyen Tassia na yankin Tilabery a jiya Talata.

Lamarin ya faru ne a misalin karfe 10 na safiyar Talata 25 Yuni a kauyen Tassia Kudu da Bandjo dake karkarar Tera a jihar Tilabery inda wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki kan dakarun gwamnati, inji sanarwar ma’aikatar tsaro wacce ta kara da cewa wasu sojoji tara sun jikkata sannan an lalata motoci biyu yayin da askarawan gwamnatin suka yi nasarar kashe ‘yan ta’adda da dama tare da lalata masu ababen hawa.

Jama’ar kasa na nuna juyayi dangane da yadda matsalar tsaro ke haddasa asarar rayukan jami’an tsaro da farar hula duk da matakan da hukumomi ke cewa suna dauka.

Gundumar Tera da ke matsayin yankin da Nijar ke iyaka da Burkina Faso na daga cikin wuraren da ‘yan ta’adda suka zafafa kai hare-hare a ‘yan watannin nan lamarin da ya tilasta wa mutane da dama neman mafaka .

Wani masani akan sha’anin tsaro Abass Moumouni na fassara lalacewar yanayin da karancin matakan hadin gwiwa saboda haka ya shawarci kasashen kawancen AES su gaggauta zartar da ayyukan rundunar da suka sanar cewa sun samar a watannin baya,

Jamhuriyar Nijar da ke kewaye da kasashen da ke fama da ayyukan kungiyoyi masu ikirarin jihadi na fuskantar hare-haren ta’addanci a yankunanta da dama musamman jihar Tilabery dake iyaka da Burkina Faso da Mali.

Hakan ya sa sojojin kasar kifar da gwamnatin farar hula a watan Yulin 2023, haka kuma sabbin hukumomin sun kori sojojin kasashen yammaci saboda zarginsu da rashin yin wani tabbas a yunkurin daidaita al’amura tare da maye gurabensu da dakarun Rasha masu aikin horo da nufin samo bakin zare, sai dai da alama har yanzu da sauran rina.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

An Fara Zaman Makoki A Nijer Bayan Wani Harin 'Yan Bindiga Da Ya Hallaka Sojoji 20.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG