A jamhuriyar Nijer masu bin diddigin al’muran yau da kullum sun fara maida martani dangane da abinda ya faru da tsohon shugaban Amurka dan takarar Republican a zaben da ke tafe Donald Trump wanne wanne harbin bindiga ya same shi a kunne lokacin da ya ke jawabi a yayin wani gangamin magoya bayansa.
Suna masu kwatanta abin a matsayin wata alamar rarrabuwar kan da ke tsakanin Amurkawa a fannin siyasa kamar yadda ake hasashen yiwuwar abin na iya zama wani mataki daga masu hamayya da takarar Trump a jam’iyarsa.
Dr Sani Yahaya Janjouna ya danganta al’amarin da koma bayan da dimokradiya ke fuskanta a cikin jam’iyyun siyasar Amurka wanda kuma a dai gefe za a iya alankanta shi da rarrabuwar kan da jama’ar kasar ke fama da ita a fannin siyasa.
A cewar Dan farar hula na gamayyar Reseau Esperance Bachar Mahaman dan jarida ne kuma masani doka wannan yunkuri, da ke tunatar da kisan da aka yi wa shugaba Kennedy a 1968, na iya haddasa zaman dar dar a wannan lokaci da yakin neman zabe ya kankama..
Kawo yanzu gwamnatin Nijar ba ta bayyana matsayi kan wannan al’amari na yunkurin kisan Trump ba yayin da sakonni shugabanin duniya ke ci gaba da karade kafafen sadarwa na zamani.
Dimokradiya da ainahi ake yi wa kirari da mulkin al’umma domin al’umma ta kama hanyar rikidewa zuwa mulkin attajirai da makusantansu sakamakon rawar da kudade ke takawa a sha’anin siyasa. matsalar da hatta kasashen da suka ci gaba ma ba su tsira ba. ya zama wajibi a yi gyara a kai don samar da daidaito a tsakanin jama’a inji Bachar Mahaman.
A saurari rahoton Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna