Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Bada Belin Wasu Ministocin Gwamnatin Bazoum


Hambararren Shugaban Kasar Nijar Mohamed Bazoum
Hambararren Shugaban Kasar Nijar Mohamed Bazoum

Wata kotu a jamhuriyar Nijar ta bada belin wasu daga cikin ministocin gwamnatin hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum bayan shafe shekara guda a tsare a gidajen yari daban-daban na jihohin Tilabery da Dosso sakamakon zargin cin amanar kasa.

Tuni ‘yan uwa da aminai suka fara murna akan wannan mataki, koda yake har yanzu ba a san takamaimiyar makomar Mohamed Bazoum da sauran mukarraban gwamnatinsa da ake ci gaba da tasrewa.

Ministoci kimani hudu daga cikin mukarraban hambararriyar gwamnati ne kotun ta bada belinsu a yammacin jiya Litinin 29 ga watan Yulin 2024 wadanda tun a washe garin juyin mulkin na Yulin bara aka tsare a gaidajen yarin Kollo Say Birnin Gaoure da Ouallam sakamakon yin tir da wannan al’amari na dakatar da tafiyar dimokradiyya a Nijar.

Lauyan dake kare wadannan tsofaffin ministoci Me Illo Issoufou ne ya tabbatar da matakin kotun.

Koda yake shi ma shugaban kungiyar MOJEN Siradji Issa ya yaba da matakin sakin wadannan ‘yan siyasa a wani gefe ya nuna bacin ransa dangane da yadda abubuwa suka faru tunda farko.

Shugaban jam’iya Foumakoye Gado da 'dan majalissar dokokin kasa, Kalla Moutari da ministan man fetur, Maman Sani Mahamadou Issoufou wato 'dan tsohon shugaban kasa da tsohon ministan ilimi, Daouda Marthe har yanzu na hannun hukumomi, amma lauya Illo na ganin akwai yiwuwar su ma a bada belinsu a nan gaba.

A rahoton da ta fitar a karshen mako dangane da abubuwan da suka wakana a tsawon shekara guda na mulkin soja, kungiyar ANLC reshen Transparency International a Nijar ta bukaci hukumomi su saki jami’an da ta ce ana tsare da su ba a kan ka’ida ba.

A yanzu haka firai ministan hambararriyar gwamnatin, Ouhoumoudou Mahamadou da ministansa na harakokin waje, Hassoumi Massaoudou da ministan kasuwanci, Alkache Alhada na hijira a waje da ma wasu manyan hafsoshin soja da hadiman fadar shugaban kasa da suka arce sa’o'i kadan bayan bayyanar labarin kifar da Mohamed Bazoum.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Wata Kotu A Nijar Ta Bada Belin Wani Rukuni Na Ministocin Gwamnatin Bazoum
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG