A yayinda ake cika shekara 1 da juyin mulkin da soja suka yi wa zababbiyar gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum ‘yan Nijar sun fara bita game da sabuwar tafiyar da hukumomin mulkin sojan kasar suka karkata kanta a fannin diflomasiya wace ta tahallaka kan raba gari da kasashen yammaci domin bai wa takwarorinsu na gabashin duniya karfi.
Kyaukyawar dangantakar dake tsakanin ECOWAS kasashen yammaci ta haddasa ficewar Nijar da kawayenta Mali da Burkina Faso daga kungiyar don kafa kungiyar AES.
Mai sharhi akan al’amuran yau da kullum Abdourahaman Alkassoum na danganta wannan kawance da yunkurin warware matsalolin tsaro.
Sai dai wani jigo a kungiyar MCPR na mai nuna gamsuwa da sabon salo.
A karkashin abinda suka kira Sabuwar tafiyar kasa, mahukuntan Nijar sun karfafa hulda da kasashen Rasha, Turkiya da Iran wadanda tun fil azal ba sa ga maciji da na yammacin duniya.
A ci gaban wannan tankiyar diflomasiya an kori sojojin Faransa har ma da jakadan kasar kafin daga bisani aka bukaci Amurka ta kwashe dakarun da ta girke a arewacin kasar da sunan yaki da ta’addanci.
A ra’ayin Shugaban kungiyar farar hula ta MOJEN Siraji Issa an fuskanci koma baya a fannin diflomasiya.
Kusancin da aka fara samu a tsakaninta da Nijar ya sa Rasha aiko da dakaru masu aikin horo hade da kayan aikin da aka ayyana cewa ta bayar ne a matsayin gudunmowar yaki da ‘yan ta’addan sahel.
Kusan ana iya cewa fannin diflomasiya na daga cikin fannonin da dambarwar juyin mulkin 26 ga watan Yuli ta yi wa tarnaki.
Domin tilasta wa sojoji janyewa daga fagen siyasa kungiyar CEDEAO ta kakaba wa Nijar jerin takunkumai tare da basu wa’adin mako 1 su mayar wa Mohamed Bazoum kujerarsa kokuma ta yi amfani da karfin soja.
Wannan mataki ya harzuka hukumomin CNSP da ma al’ummar Nijar. An shafe watanni kusan 6 ana kai ruwa rana kafin a karshen watan Janairun da ta gabata, Nijar da Mali da Burkina Faso su bada sanarwar ficewa daga kungiyar da suke zargi da zama ‘yar amshin shatan Faransa.
Kasashen 3 wadanda ke karsahin mulkin soja da tuni suka kafa kungiyar AES sun yi watsi da dukkan wani tayin mayar da su sahun dangi duk kuwa da cewa ta janye takunkumin da ta kakaba. Suna masu cewa bakin alkalami ya rigai ya bushe.
Shugaban Najeriya da na Benin da na Cote d’ivoire sun fuskanci suka daga wajen jama’a saboda zarginsu da yin gaba gaba wajen kushe juyin mulkin da aka yi a Nijar. Lamarin da ya sa a yanzu haka iyakar kasar da Benin ke rufe. To amma idan aka yi la’akari da yadda ‘yan ta’adda ke yada aiyukansu a yankin Afrika ta yamma dole ne AES da CEDEAO su kalli juna da idon rahama.
Bankin duniya da asusun IMF wadanda a washegarin juyin mulkin 26 suka dakatar da aiyukansu a Nijar sun dawo kasar da nufin dorawa daga inda suka tsaya yayin da kasashen gabashi suka dukufa da zawarcin lasisin hakar ma’adanai da aka karbe daga hannun wasu kamfanonin kasashen yammaci da ake zargi da gaza mutunta yarjejeniyoyin da suka saka hannu kansu a baya.
Kasashen yammacin duniya da kungiyoyin kasa da kasa irinsu EU da MDD wadanda a bisa nasu manufofin ba su laminci a kwaci mulki da karfin bindiga ba sun yi ta matsin lamba ga sojojin CNSP su mayar da hambararen shugaban kasa kan mukaminsa abin da sabbin hukumomin na Nijar suka ce ba za ta sabu ba , suna mai cewa irin wannan matsayi na kasashen Faransa da Amurka da kawayensu tamkar katsalandan ne a harkokin wata kasa mai cin gashin kanta.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna