Dalilin haka shi ne, lauyan gwamnati a wannan shara’a mai nasaba da zargin cin amanar kasa ya sake daukaka kara da nufin ci gaba da binciken da ya kaddamar kan wadanan fursinonin ministoci.
A yayin zamanta na farko na wannan shekara da ta gudanar a tsawon makwanni biyu kotun Tribunal Militaire ta nazarci da dama masu nasaba da zargin aikata laifikan soja, a karkashin mai shara’a Moussa Waziri wanda yake shugaban wannan kotun.
Daya daga cikin batutuwan da suka dauki hankula a wannan zama shine makomar tsofaffin ministocin gwamnatin hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum wadanda a farkon makon nan sashen daukaka kara na kotun ya bada belin hudu daga cikinsu da suka hada da Hama Souley Adamou da Ahmed Djidoud da Rabiou Abdou da Ibrahim Yacouba sai dai zancen nan da ake ana ci gaba da tsare su.
Ko baya ga wadanan ministoci, makomar sauran takwarorinsu da ke tsare tun a washegarin juyin mulkin na 26 ga watan Yulin 2023 abu ne da ke janyo aza ayar tambaya daga wajen jama’a.
Kawo yanzu lauyoyin wadanan ‘yan siyasa ba su bayyana matsayinsu ba dangane da kiki-kakar da ake fuskanta game da batun zartar da umurnin da kotun ta bayar a ranar Litinin 29 ga watan Yulin 2024.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna