Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu A Nijar Ta Sako Wani ‘Dan Jarida Bayan Ya Shafe Watanni Uku A Gidan Gyara Hali


Wata kotu a Nijar ta bada belin wani ‘dan jarida bayan da ya shafe watanni kusan uku a gidan yari saboda zargin yi wa sha’anin tsaron kasa karan tsaye.

Soumana Idrissa Mai dai ya ruwaito labarin da ke nuna hasashen yiwuwar jami’an Rasha sun kafa na’urorin sauraren jama’a a manyan gidajen gwamnati a birnin Yamai da nufin bai wa hukumomin mulkin sojan kasar damar tatsar bayanai a asirce.

A ranar 29 ga watan Afrilun 2024 alkali mai bincike ya tura mawallafin jaridar L’Enqueteur Soumana Idrissa Maiga gidan yari bayan da ya shafe kwanaki hudu a hannun ‘yan sandan farin kaya.

A fitowarta ta ranar 25 ga watan Afrilu jaridar ta ruwaito cewa ‘’ana hasashen jami’an Rasha sun kafa na’urorin sauraren jama’a akan manyan gidajen gwamnati’’. Shin wa ake zubawa ido kuma saboda me aka yi haka?

Mafarin kama ‘dan jaridar ke nan a bisa zarginsa da yi wa sha’anin tsaron kasa barazana.

Bayan zaman wakafi na watanni kusan uku alkali ya bada belinsa a matsayin sakin talala.

Daya daga cikin mukarraban jaridar ta L’Enqueteur Amadou Harouna dake farin ciki kan sakin maigidansu ya bayyana cewa ‘’abu ne da ba a taba gani ba saboda ‘dan jarida ya kwofi labari daga wata jarida a kama shi.

Dokokin aikin jarida a Nijar sun hana garkame ‘dan jarida a kurkuku saboda dalilai masu nasaba da aikinsa saboda haka shugaban kungiyar ANEPI ta mawallafan jaridu masu zaman kansu Zabeirou Souley ya gargadi hukumomi da ma ‘yan jarida akan maganar mutunta dokoki da ka’idojin wannan fanni.

A yayinda ‘yan uwa da abokai ke murnar fitowar mawallafin jaridar l’Enqueteur, alkalin kotu ya yanke wa Intinicar Alhassan hukuncin dauri na watanni 12 a kurkuku tare da biyan tarar million 5 na cfa.

Ana zargin wannan ‘dan siyasa da laifin yada kalaman batanci bayan da ya wallafa wasu bayanai a kafar sada zumunta dangane da kisan wasu magidanta a jihar Tilabery.

Sai dai launyansa Maitre Lirwana Abdourahamane ya ce ba su gamsu da hukuncin ba saboda haka zasu garzaya kotu ta gaba.

Intinicar Alhassan wanda ya fada hannun hukumomin Nijar a ranar uku ga watan Yunin da ya gabata na daya daga cikin masu sukar lamirin gwamnatin mulkin soja ta CNSP, haka kuma ya na daga cikin daidakun mutanen da a fili ke nuna goyon baya ga hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

 Gwamnatin Nijar Ta Sako Wani ‘Dan Jarida Bayan Ya Shafe Watanni Uku A Gidan Gyara.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG