Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fursunoni Sun Gudu A Wani Gidan Yarin Jamhuriyar Nijar


Wani ‘dan Najeriya mai gadi a wajen gidan gyara hali na Koutoukale, Nijar
Wani ‘dan Najeriya mai gadi a wajen gidan gyara hali na Koutoukale, Nijar

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun karfafa matakan tsaro a gundumar Tilabery da nufin farautar fursunonin da suka arce a ranar Alhamis da la’asar daga gidan yarin Koutoukale mai tazarar kilomita 50 daga babban birnin Yamai.

Kawo yanzu ba a bayyana yawan wadanda suka gudu ba a yayin da ma’aikatar cikin gida a wata sanarwa ta umurci daukacin gwamnoni da shugabanin kananan hukumomin kasar da sarakunan gargajiya da shugabanin addinai da su dauki matakan zuba ido tare da fadakar da al’umma kan bukatar sanar da ma’aikanta da zarar an lura da bakuwar fuska.

Mummunar tarzomar ce aka ayyana cewa ta barke a gidan kason Koutoukale cikin yanayin ba-za-ta a kurkukun da ke daya daga cikin mafi tsauraran matakan tsaro a Nijar.

Wannan gidan yari wuri ne da ake tsare da ‘yan ta’adda da masu safarar miyagun kwayoyi da makamai da gaggan ‘yan ta kife.

Ya zuwa wannan lokaci ba a bayyana adadin wadanda suka sha ba koda yake, wasu rahotannin da babu tabbas kansu na cewa an debi makamai da motoci.

Tuni hukumomi birnin Tilabery suka kafa dokar hana fita daga karfe 9 na dare zuwa 6 na safe matakin da jim kadan aka fadada shi zuwa ilahirin garuruwan gundumar da zummar hana mutane shiga daga wasu yankunan na daban.

Shugaban kungiyar Conseil Eleveurs Nord Tilabery ta makiyayan arewacin jihar Tilabery Boubacar Diallo ya gargadi jama’a da su bada hadin kai.

A shekarar 2016 da 2019 ma an yi barin wuta a gidan yarin Kououtoukale lokacin da aka kai wasu hare-haren da aka dora alhakinsu a wuyan ‘yan ta’adda a matsayin yunkurin fitar da mutanensu daga kurkuku, to sai dai abin da ya wakana a wannan karon masana sha’anin tsaro na cewa abu ne da ke da alamar hazo tattare da shi.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto hukumomi ba su yi karin bayani ba kan abubuwan da suka biyo bayan matakan da suka dauka daga faruwar wannan tarzoma ta la’asariyar Alhamis zuwa yau Juma’a.

Gidan yarin Koutoukale dai mai daruruwan fursunoni na da ta’azarar kilomita 50 da birnin Yamai ne kuma kilomita 110 da Tilabery babban birnin jiha.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Tarzoma A Wani Gidan Yarin A Nijar Ya Yi Sanadin Tserewar Fursunoni Galibi 'Yan Ta'adda.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG