Matakin da tuni ‘yan kasa suka fara nuna farin ciki akansa, koda yake wasu na kwatanta abin a matsayin yunkurin cimma wata manufar siyasa.
Matakin, kamar yadda sakatariyar shugaban majalissar CNSP ta sanar, ya shafi man fetur na Essence da aka yi wa ragin 41fcfa wato dala 8 na cfa da tamma 1 ga kowace lita sai man Diezel na Gazoil wanda aka yi wa ragin 50 fcfa, ma’ana dala 10 na kudaden cfa.
Litar man fetur da a baya ke 54 cfa za a fara sayar da shi kan 499fcfa yayinda litar Gazoil kokuma Diezel dake 638fcfa za a fara sayar da shi kan 618 fca.
Daga ranar 23 ga watan Yulin da muke ciki ne za a fara zartar da sabon farashin a ko ina a fadin kasar kuma sanarwar hukumomin ta jaddada cewa shugaban majalissar CNSP na jiran ganin ‘yan kasuwa da masu ayyukan sufuri sun yi la’akari da wannan mataki don ganin a na su bangare sun sassauta farashin ababen masarufi da na motocin jigila.
Shugaban kare hakkin masaya ADDC WADATA Mahaman Nouri na ganin yiwuwar sabon farashin man zai bada damar rage kudaden jigila.
Ganin yadda abin ke zuwa a lokacin da ake gab da cika shekara 1 da juyin mulkin da ya bai wa majalissar CNSP damar dare karagar mulkin Nijar ya sa wasu ‘yan kasar ke kallon matakin rage farashin man tamkar wani yunkurin cimma manufofin siyasa ne.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna