Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Shi'a Sun Yi Tattaki Albarkacin Ranar Ashura


Sallar Ashura a Nijar
Sallar Ashura a Nijar

Yayinda al’ummar Musulmi a kasashe daban daban ke shagulgulan sallar Ashura a yau talata 10 ga watan Muharram, ‘yan shi’ah sun yi tattaki a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar domin nuna juyayi akan kisan Imam Hussein, daya daga cikin jikokin annabi Muhammad S.A.W. da aka yi a Karbala dake kasar Iraqi.

Da yake jawabi a albarkacin wannan rana shugaban ‘yan Shi’a na kasa Sheik Salissou Ahmed Lazaret ya gargadi shugabanin duniya akan kwatanta adalci a tsakanin jama’a domin, a cewarsa, rashin yin hakan na kan gaba a jerin dalilan rigingimun da ake fama da su a kasashe da dama.

Jigo a kungiyar fafutika ta Sauvons le Niger Salissou Amadou da ke bayyana ra’ayinsa na cewa wajibi ne al’umma tallakawa su dawo kan hanyar gaskiya.

Karancin adalci a sha’anin shari’a kokuma rashinsa kwata kwata a galibin kasashen duniya, shine mafarin halin da ake ciki a yau, saboda haka wajibi ne a dauki matakai kan halin da fannin ke ciki muddin ana son shimfida adalci a tsakanin jama’a inji Hamidou Sidi Foddy na kungiyar kulawa da Rayuwa.

Ranar Ashura, 10 ga watan Muharram, rana ce mai muhimmanci ga duk Musulman duniya.

Wasu bangaren Musulmai su na gudanar da azumi a wannan rana domin kwatanci da Annabi (SAW). Amma ga ‘yan Shi’a, rana ce ta jimami domin kisar da aka yi wa Imam Hussaini, jikan Annabi (SAW), a Karbala a shekarar 680 Miladiya.

'Yan Shi'a Sun Yi Tattakin Ranar Ashura a Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG