Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Kasashen Kungiyar AES Sahel Za Su Gudanar Da Taron Koli A Yamai


Tutocin kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso
Tutocin kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso

Shugabanin gwamnatocin mulkin sojan Burkina Faso, Mali da Nijar na shirin gudanar da taronsu na farko a karkashin inuwar kungiyar AES a ranar Asabar 6 ga watan Yuli a birnin Yamai.

Taron dai na da nufin jaddada hadin kan da ke tsakanin kasashen uku ne bayan da a watan Janairun da ya gabata suka fice daga kungiyar ECOWAS.

Wadanan Kasashe na fama da aika-aikar kungiyoyin ta’addanci saboda haka babbar maganar kudaden bai daya taron zai tattauna hanyoyin da za’a tunkari wannan lamari da ke haddasa kisan dimbin jami’an tsaro da fararen hula.

Sanarwar fadar shugaban majalissar CNSP na cewa kaftin Ibrahim Traore na Burkina Faso da Kanal Assimi Goita na Mali zasu sauka birnin Yamai da la’asariyar wannan Juma’a a albarkacin taron koli na farko na shugabanin kasashen AES da zai gudana a gobe asabar.

Tare da mai masaukin baki Janar Abdourahamane Tiani na Nijar wadanan shugabanin gwamnatocin mulkin soja zasu tattauna akan matsalolin da ke addabar kasashen uku.

A watan Fabrairun da ya gabata ne ministoci daga kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso a karshen taron da suka gudanar a Ougadougou suka shawarci shugabanin kasashen su yi nasu taron don jaddada abubuwan da suka tsayar mafarin wannan haduwa ta Yamai da zai kasance lokaci na saka hannu kan takardun tabbatuwar hadin kai ta yadda zasu kasance masu manufofi guda. Abinda Mahamadou Tchiroma AIssami jigo a kungiyar ROTAB ya kira ci gaba a kokarin ‘yantar da yankin Sahel.

Batun kudaden bai daya na kasashen Sahel na daga cikin abubuwan da wadanan shugabanni zasu tsaida magana a kansu kasancewarsa daya daga cikin igiyoyin da ake zargin Faransa na ci gaba da amfani da su don jan zarenta a wajen kasashen da ta yi wa mulkin mallaka.

Nijar, Mali da Burkina Faso sun fada karkashin mulkin soja sakamakon lalacewar al’amuran tsaro inda kungiyoyin ta’addanci ke yada aiyukan da ake zargin kasashen yammaci da hannu wajen kitsawa.

Kasashen uku dai sun fice daga CEDEAO a watan Janairun 2024 saboda zargin shugabaninta da kaucewa manufofin kungiyar. Sannan sun kafa rundunar hadin guiwar AES a watan maris din da ya gabata da zummar tunkatar kalubalen tsaron da ke haddasa mutuwar sojoji da fararen hula a kowacce daga cikinsu.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Shugabannin Kasashen Kungiyar AES Sahel Za Su Gudanar Da Taron Koli A Yamai
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG