Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Nijar Ya Zargi Najeriya, Jamhuriyar Benin Da Bai wa Jami'an Faransa Masu Leken Asiri Mafaka


Abdourahamane Tiani
Abdourahamane Tiani

Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar ya bayyana damuwa dangane da yadda ya ce Najeriya da Jamhuriyar Benin suka bai wa wasu jami’an leken asirin Faransa mafaka da nufin shirya wata makarkashiya a yunkurinta na haddasa tashin hankali.

Janar Abdourahamane Tiani a hirarsa ta kafar talbijan RTN a albarkacin zagayowar ranar samun ‘yancin kai ta 3 ga watan Agusta karo na 64 ya ce suna da kwararan hujjojin da ke gaskanta wannan zargi.

A cewar Janar Tiani wasu bayanan sirrin da suka tattara ne suka tabbatar wa hukumomin mulkin sojan kasar cewa har hanzu Faransa ba ta janye kudirinta na ganin ta yi amfani da wasu kasashe makwabta don cimma burinta na haddasa hatsaniya a Nijar.

Ya kuma kara da cewa wasu bayanan na daban daga jamhuriyar Benin na nuna alamun shirin kitsa wata mummunar aniya duk kuwa da cewa iyakar kasashen biyu na rufe.

A wani bangare na wannan yunkuri da Faransa ta sa gaba tun bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023, shugaban majalissar ta CNSP ya ce sun gano karin sirrin boye masu cike da wasu bayanan fallasa.

Kawo yanzu dai ba wani martani daga gwamnatocin kasashen nan uku da Janar Abdourahamane Tiani ke zargi da yunkurin haddasa fitina a Nijar.

Yayinda ofisoshin jakadancin Faransa da na Benin a wannan kasa ke rufe yunkurin jin martanin ofishin jakadancin Najeriya ma bai yi nasara ba domin wani jami’in diflomasiyar kasar da Muryar Amurka ta tuntuba ya ce ba zasu yi magana akan wannan al’amari ba sakamakon darajta babbar alakar al’umomin kasashen biyu masu al’adu da addinai da komai na zamantakewa iri daya.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Shugaban Nijar Ya Zargi Najeriya Da Jamhuriyar Benin Da Baiwa Jami'an Faransa Masu Leken Asiri Mafaka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG