Ministan Zongo a Ghana, Ben Abdallah Banda ya tsokaci a game da cikar Muryar Amurka shekara 45 da kafuwa.
A Yamai na jamhoriyar Nijar, Abdourahamane Mai Hula, wanda ya ke cikin masu sauraren sashin Hausa na Muryar Amurka tun lokacin da aka bude shashin shekaru 45 da suka gabata, ya yi tsokaci game da cikar Muryar Amurka shekara 45 da kafuwa.
Najeriya ta ce hukumomin sojin kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso wadanda ba zababbun al’umman kasar ba ne sun zalunci al’ummarsu yayin da su ka dauki matakin hadin gwiwa na ficewa daga kungiyar ECOWAS.
Wasu da ake zargin mayakan IS ne sun kashe mutane 22 a hari da suka kai a wani kauye da ke yammacin Jamhuriyar Nijar kusa da kan iyaka da Mali, kamar yadda wasu majiyoyi na cikin gida suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa a ranar Litinin.
Manyan kasashe masu ba da agaji da dama sun ce za su dakatar da bayar da kudade ga hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Falasdinu ta Majalisar Dinkin Duniya, biyo bayan zargin da Isra'ila ta yi na cewa ma'aikatanta na da hannu a harin da kungiyar Hamas ta kai ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ko CEDEAO ta mayar da martani kan sanarwar ficewar kasashen Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar daga cikinta.
A lokacin da wakilan shugaban kasar Venezuela Nicolás Maduro da jam'iyyun adawa da dama na Venezuela da ake kira Unitary Platform, suka rattaba hannu kan yarjejeniyar da aka fi sani da yarjejeniyar Barbados a watan Oktoba.
Bisa bayanan WHO, wasu jerin bincike da aka gudanar sun nuna cewa ganyen tabar wiwi yana da tasiri a fannin maganin cututtuka daban-daban, daga cikin su, har da yanayin tashin zuciya da ammai.
An kama shi a watan Afrilun 2023 bayan da aka gano gawarwakin mutane a dajin Shakahola da ke kusa da tekun Indiya.
HRW ta ce ta yi hira da shaidu da dama tsakanin watan Satumba zuwa Nuwamba tare da tantance hotuna, bidiyo da hotunan tauraron bil adama.
A ranar Laraba, wasu tankokin yaki guda biyu sun kai hari a matsugunin Majalisar Dinkin Duniya a Khan Yunis inda dubban Falasdinawa da suka rasa matsugunansu suka fake.
A ranar Laraba ne Shugaban mulkin sojin Chadi, Mahamat Idriss Déby ya isa birnin Moscow da ke Rasha domin ganawa da Shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin a fadar Kremlin.
Dan shekaru 79 da haihuwa ya doke tsohon dan wasan kwallo, wadda ya taba lashe kyautar Ballon d'Or, George Weah a zagaye na biyu na zaben watan Nuwamba da kashi 50.64 na kuri'un da aka kada.
Mai shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya soke kasafin Naira biliyan 800 da kungiyar ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas karkashin jagorancin Edison Ehie ta amince da shi da kuma sanya hannun gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara.
Duk da matakai da ake cewa ana dauka don samar da tsaro, ana ci gaba da samun matsalar satar mutane don kudin fansa a wasu sassan kasar, ciki har da Abuja babban birnin tarayyar kasar.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayana cewa kasar Cape Verde ta yi nasarar kawar da cutar Malariya. Kasar ta zama ta 3 a nahiyar Afirka da aka tabbatar da nasasrar kawar da cutar bayan kasar Mauritius a shekara ta 1973 da Algeriya a 2019.
Za ta kafa tarihi a watan Mayu, bayan da abokan aikinta baki danayansu suka zabe ta a matsayin Magajiyar garin Leeds a Burtaniya.
Kungiyar ta Houthi ta ce suna nuna goyon bayansu ga Falasdinawa ne a daidai lokacin yakin da Isra'ila ke yi da mayakan Hamas a Gaza kuma sun kai hare-hare fiye da 30 a tekun Bahar Rum.
Solangi ya ce manufar taron ita ce yin nazari mai zurfi kan harkokin tsaron kasa bayan abubuwan da suka faru a Iran da Pakistan.
Masu aikin ceto sun kwaso gawarwaki bakwai daga cikin laka, ciki har da na yara. Wasu mutane hudu kuma har yanzu ba a gansu ba, Rocris Idul ya shaida wa AFP.
Domin Kari